Sarkin Bichi ya yi wa hukumar kwana-kwana nasiha

Sarkin Bichi ya yi wa hukumar kwana-kwana nasiha 

Daga Hassan Muhammad

Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ao Bayero ya yi kira ga Hukumar kashe gobara ta kasa da su kara kaimi wajen cim ma nasarar ayyukansu, musamman wajen wayar da kai da hana aukuwar gobara.kin 

Mai martaba ya yi wannan kiran ne, a lokacin da shuga­bannin na kasa suka kai masa ziyara, a makonni biyu da suka gabata.

Ya ce, aikinsu bai tsaya wajen kashe gobara ba, har ma da ceto rayukan al’umma, don haka ya kamata su kara kaimi wajen tabbatar da matsalolin da ke addabar Hukumar, cikin wannan yanayi na damina.

A nasa jawabin, shugaban tawagar ya bayyana cewa, sun zo fadar ne domin sanar da Sarkin ire-iren ayyukan hukumar.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: