Kan saba ka’ida: Chadi ta dakatar da buga jaridun kasar 12

Kan saba ka’ida: Chadi ta dakatar da buga jaridun kasar 12

Hukumar tace labarai a kasar Chadi ’Hama’, ta dauki matakin dakatar da wadansu jaridun kasar 12 har tsawon watanni uku saboda saba wa ka’idar ayyukansu.

Hukumar da ake kira Hama ta ce jaridun 12, sun gaza cika sha­rudan da aka gindaya wa kafafen yada labarai a karkashin sabuwar dokar da ta fara aiki tun a shekara ta 2018.

Wadansu daga cikin sharuddan sun hada da cewa, dole ne shuga­ban kamfanin wallafa laba­rai ya kasance kwararren dan jarida da ke da matsa­yin ilimi na akalla shekaru biyu a jami’a ko kuma wata babbar makaranta maka­manciyarta.

Bayan share watanni uku ba tare da sun cika wannan ka’ida ba, hukumar ta ce za sanar da sabon hu­kunci a kan wadannan ja­ridu. To sai dai Mad Laoun­gar, shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan’adam na kasar LTDH, ya zargi mahukunta da ne­man haddasa tarnaki ga ai­kin jarida a kasar.

Biyar daga cikin jaridun na fitowa ne da harshen far­asanci, su ne le Haut Parleur, le Baromètre, la Sugges­tion, le Potentiel da kuma Lalakoum, sai sauran da ake bugawa da harshen lar­abci su ne, Tchad Al yaum, Alnada, Shaba Tchad, Al Khabar, Al Ayam, Al Haya da kuma Atihad.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: