Jamus, Rasha na gab da sanya zare- Saboda sabani

Jamus, Rasha na gab da sanya zare- Saboda sabani

 Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce, ana iya samun matsala a ai­kin shimfida bututun iskar gas na Nord Stream 2 idan Rasha ta gaza gudanar da bincike a game da shayar da jagoran ‘yan adawan

kasar, Aledei Nabalny Guba.

Yayin da aka tambaye shi ko uwargida Merkel za ta kare aikin shimfida bututun iskar gas na biliyoyin Yuro daga Rasha zuwa Turai, ka­kakin shugabar Jamus Stef­fen Seiber ya ce, shugabar ta yi amannar cewa, ba zai ky­autu a yanke wani hukunci ba a yanzu.

Aikin shimfida bututun iska gas na Nord Stream 2, na kudi Yuro biliyan 10, wanda ake gab da kammala shi, ana yin sa ne da zummar ribanya iskar gas da Rasha ke tura wa Jamus.

Da ma can Amirka na dari-dari da aikin, inda har ta caccaki kasashen Turai da dogaro da ya wuce kima a kan makamashi daga Rasha.

Ko a tsakanin kungiyar Tarayyar Turai, akwai ka­sashen da ke adawa da aikin shimfida bututun iskar gas din, ganin cewa, Poland da sauran gungun kasashen ga­bashin Turai ke nuna farga­bar kada dogaro da iskar gas daga Rasha ya zarce kima.

Sai dai duk da bambancin ra’ayi a siyasance a tsakanin­ta da Rasha, Jamus na ganin aikin shimfida iskar gas din wata hanya ce ta tabbatar da samun tsayayye, kuma tsabtataccen makamashi a yayin da take janyewa daga amfani da makamashin kwal da nukiliya.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: