A Sakkwato:  Zaben PDP ya bar baya da kura

A Sakkwato: Zaben PDP ya bar baya da kura 

Musa Lemu Daga Sakkwato

Zaben shugabannin jam’iyya na kananan hu­kumomi wanda aka gu­danar a jihar Sakkwato a kwanan­nan ya bar baya da kura.

 

Zaben ya jawo ce-ce ku-ce a tsakanin yan takara da sauran magoya baya da suke ganin cewa an yi ba dai dai ba a inda hakan ya san ya wasu daga cikin yan ta­karar suka rubuta takardar korafi, suka mika ta ga shugaban jam iyyar PDP na jihar da kwamitin da jam iyya ta kafa domin duba matsalolin .

A yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala zaben Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba yace jam’iyyarsa ta gu­danar da zabubbuka cikn lumana da kwanciyar hankali .

Ayayin da yake zantawa da manema labarai daya daga cikin yan takarar shugaban karamar hukumar Sakkwato ta Arewa Al­haji Kasimu Ummarun Kwabo yace sam basu gamsu ba kuma basu amince da zaben da aka gu­danar ba.

Alhaji Kasimu Umma­run Kwabo ya ce shugabannin jam’iyya sun yi yadda suke so bayan da gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa, a bai wa kowa hakkinsa domin sa­mar da zama Lafiya da ci gaban jihar Sakkwato.

Ya ce ganin yadda aka yi ba dai dai ba ta hanyar zalunci ya sanya suka rubuta takar korafin kuma suka mika ta ga shugaban jam’iyyar na jihar da kwamitin da jam iyya ta kafa .

A yayin da manema Labarai suka tuntubi shugaban jam iyyar PDP na jihar Sakkwato Alhaji Ibrahim Mil goma ya tabbatar cewa sam sam bai karbi wata ta­karda ta korafi daga kowane dan jam’iyya ba, a saninsa anyi zabe lafiya an kare lafiya .

Alhaji Ibrahim Mil goma ya ce zabe akan sami nasara ko fadu­wa a saboda haka duk wanda ya fadi zabe sai ya rungumi hakuri

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: