Sheikh Nazifi ya zama shugaban Da’iratil Anwar na Kaduna

Sheikh Nazifi ya zama shugaban Da’iratil Anwar na Kaduna 

Isa A. Adamu Daga Zariya 

 

Fitaccen malamin add­inin musuluncin nan da ya shafe shekaru da dama ya bayar da gudun­muwarsa wajen koyarwa da kuma yin wa’azi a karamar hukumar Zariya da kuma jihar Kaduna a karkashin kungi­yar DA’IRATIL ANWAR, FI – MADAHIL SAYYADIL ABBARAR [ S.A.W. ], Shekh Nazifi Ahmad Bawa ya zama sabon shugaban wannan kungiya na jihar Kaduna.

 

Shekh Nazifi Ahmad ya sami damar zama shugaban wannan kungiya ce, bayan ra­suwar tsohon shugaban kungi­yar Shekh Sharu Salisu Kusfa a watannin da suka gabata.

A zantawar da Shekh Na­zifi ya yi da wakilinmu jim kadan bayan daukacin ‘ya’yan kungiyar sun gudanar da taro a Zariya da suka tabbar ma sa da wannan kujera, ya nuna matukar jin dadinsa da wan­nan dama da ‘ya’yan kungiyar suka ba shi, na ya ci gaba da shugabancin kungiyar daga wanda ya gada, marigayi Shekh Sharu Salisu Kusfa, Ya yi amfani da wannann dama, inda ya yi addu’o’I na musamman ga tsohon shuga­ban kungiyar marigayi Shekh Sharu Salisu Kusfa na dinbin gudunmuwar day a bayar na ganin wannnan kungiya ta sami daukaka da kuma samun damar ciyar da al’ummar mu­sulmi gaba da kuma musulunci gaba ta fannonin karantarwa da kuma wa’azi a sassa daban – daban na jihar Kaduna.

Shekh Nazifi, ya yi kira ga daukacin ‘ya’yan kungiyar da su ba shi duk goyon bayan da suka kamata, domin ya sami saukin samun damar dau­kar shugabancin da aka dora ma san a shugaban wannan kungiya na jihar Kaduna baki daya.

Da kuma Shekh Nazifi Bawa ke tsokaci kan matsalo­lin rashin hadin kai a tsakanin al’ummomin musulmi, ya shawarce da su lura da cewar, matsalolin da suke tasowa daga wadanda ba musulmi ba, na yadda ba sa zaben mu­sulmin da za su durkusar a sassan duniya, ya ce ya dace al’ummar musulmi da su ke jagorantar kungiyoyin add­inin musulunci, su ci gaba da karatun ta – natsu, domin kawo karshen matsalolin da suken addabar musulunci da kuma musulmi baki daya, ban an Nijeriya kawai ba.

A dai zantawrsa da wakilinmu Shekh Nazifi ya bukaci gwamnatoci da su ci gaba da ba malaman addi­nai duk goyon bayan da suka kamata, a batun yin addu’o’I a kasa da kuma su kan su shugabannin, kamar yadda ya ce, a shekarun baya, shuga­bannin da suka gaba, sun yi bakin iyawasu, na ganin sun nuna muhimmancin yi wa kasa addu’o’I dare da rana.

Karshe, Shekh Nazifi Ah­mad Bawa ya yi addu’o’I na musamman ga mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Id­ris, na yadda ya rungumi wan­nan kungiya da hannu biyu tun daga lokacin da aka kafa ku giyar ya zuwa wannan lokaci, sai ya ce, ya na fatan sauran shugabannin za su rika koyi da maimartaba Sarkin Zazzau, na rungumar kungiyoyin addini da hannu biyu tare da saurar­onsu, a duk lokacin da bukatar haka ta taso wa kungiyoyin.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: