Ina alfahari da mutanen Gezawa –Hakimi

Ina alfahari da mutanen Gezawa –Hakimi 

Daga Salihu S. Gezawa 

 

Sarautar Mundubawa, sarautace ta Fulani, Mundubawa wadda za mu iya cewa, tana kan gaba wajen kammaluwar tarihin masaurautar Kano, bayan jihadin Shehu Usman Dan­fodiyo Mujaddadi, kamar yadda muka sami zarafin tat­tauna wa da mai girma mai Unguwar Mundubawa kuma Hakimin Gezawa da ke jihar Kano Alhaji Mahmud Aminu Yusufu kamar haka:-

ALBISHIR: Allah ya kara maka Imani, za mu so mu ji tarihin sarautar ku ta Mundubawa daga bakinka?

MAI UNGUWAR MUN­DUBAWA: Alhamdulillahi Assalamu Ala Sayyadina Ra­sulillahi SAW kamar yadda ka tambayeni tarihin wannan sarauta ta mu da muka gada tun kakannin kakannin mu.

Ita wannan sarauta ta fara ne daga baya watau bayan ji­hadin Shehu Usmanu, wanda Fulanin Mundubawa suka taka rawar gani sosai kuma a cikinsu bayan an karbo tuta daga wajen Shehu Usman sai aka bai wa Sarki Suleiman (watau ainihin tushen iyay­enmu) ya zama jagora watau Sarkin Kano.

Ina nufin shi sarkin Kano Suleiman yana da ‘yan uwa su Malam Jamo amma sai suka ce shi ne karami amma shi za mu bi.

Daga nan Sarkin Kano Suleimanu ya ci gaba da Sarautar Kano har zuwa ra­suwarsa, inda kuma Sarkin Kano Dabo ya zama Sarki, inda cikin hikimar Ubangiji har yanzu zuri’arsa ce Sarau­tar Kano wanda su kuma Sul­lubawa ne.

ALBISHIR:- To, ranka ya dade ida na fahimce ka ku kun fito daga zuri’ar Sarkin Kano Suleimanu?

Mai Unguwar Munduba­wa:- Kwarai kuwa ai kamar yadda na gaya maka ne shi Sarki Suleimanu da muka fito, ai bayan Sarkin Kano Dabo ya zama Sarki daga baya sai aka yi wa zuri’ar sarautar Mai Unguwar Mun­dubawa, kuma abin da zan iya tuna wa akwai shi Jar­mai Musa, dan Santali Sani shi ma ya yi Sarauta sai ba­bansa shi ma ya yi Sarauta da Galadiman Kano sai dan Sarkin Kano Suleimanu.

Daga nan abin ya tafi har yazo kan Mai Unguwa Ama­du Gurama wanda shi yaya ne ga Mai Unguwa Yusufu mahaifi ga Alhaji Sani Geza­wa, shi ma ya yi Mai Ungu­war Mundubawa, ina nufin shi Amadu shi ne mahaifin Sani Gezawa, kuma yaya ga Mai Unguwa Yusufu Yauwa.

To daga Amadu, wanda ya koma Danlawar sai aka yi wa Mai Unguwa Yusufu Sarauta mahaifi ga mahaifi na kenan watau kakana ke­nan wanda kabarinsa yana nan a nan Gezawa bayan gi­dan Na’ibi, shi Mai Unguwa Yusufu an nada shi ne Mai Unguwa Amadu shi ya fara zama a Gezawa a matsayin mai Unguwar Mundubawa kuma Hakimin Gezawa ku­san in ce 1903 ko 1905 loka­cin Sarkin Kano Abbas, dan shi Amadu, amini ne ga Sar­kin Kano Abbas.

Dan yana nan a Gezawa ma aka yi wani abu, watau Sarkin Dutse na wancan lo­kacin yazo ya sami Sarkin Kano Abbas, ya ce ran Sarki ya dade ba na son ba ta zu­munci amma ‘yan uwana sun matsamin domin haka na hakura da Sarautar nan, ran Sarki ya dade a sami wanda ake so a nada.

Sarki ya ce, ina mai Un­guwar Mundubawa Amadu? Ya ce ran Sarki ya dade gani ya ce za ka je Dutse za ka iya? Ya ce Allah ya taimaki Sarki ko kawunan mutanen Dutse kake so zan kawo maka su.

To a nan sai Sarkin Kano Abbas ya ce, to amma ba za ka ke Mai Unguwar Mundu­bawa ba, saboda haka sai aka yi masa Dan Lawan aka kai shi Dutse kuma ya rike sosai.

A lokacin sai ya kawo kaninsa Mai Unguwa Yusufu sai aka yi masa Mai Ungu­war Mundubawa aka kai shi Gezawa. Su zuri’ar mu tun daga kan shi Amadu sun ci gaba da zama a Gezawa ka ga sun zama ‘yan gida duk an sami wadansu sun zauna sun yi Sarauta kuma ba na mu bane kamar su Dan Lawan, Dan Ruwata da sauransu.

Amma daga shi Yusufu sai wansa Mai Unguwa Adu ya gaje shi (duk uwarsu daya ubansu daya) da Mai Ungu­wa Abdu ya rasu sai dansa Mai Unguwa Inuwa ya gaje shi, shi kuma mai Unguwa Inuwa wani abu na kaddara ya faru ya bar Sarauta. Watau aka raba shi da Sarauta 1940 wani abu ne dai abin ya faru.

Daga nan sai wani dan gidan sarautar Kazaure ya zo ya zauna ba dai zuri’ar mu daya ba, amma ya zauna ya yi Sarauta har dai zuwa lo­kacin da Sarkin Kano Sanusi (Halifa) ya bar Sarauta wajen 1963 sai kuma aka nada Sani Gezawa a matsayin Mai Un­guwar Mundubawa, amma shi bai zauna a Gezawa ba ina ganin Hakimin waje ya yi har kuma ya fada siyasa ya kai matakai daban-daban.

Shi Sani Gezawa kenan iyayenmu ne, da ya shiga siyasar ya yi Kwamishina a Kano da sauran mukamai a matakin kasa, domin shi ne shugaban hukumar NEPA na farko da dai sauransu.

Daga nan sai aka yi wa mahaifi na Mai Unguwar Mundubawa Aminu Yusufu Sarauta a tsakanin 1975- 1976 ya zauna a Gezawa har tsawon shekaru 43 yana sarautar Gezawa kuma ya rasu a nan Gezawa aka binne shi a inda Kabarin mahaifin­sa yake a nan Gezawa ya rasu a shekara ta 2019, ni kuma Allah ya kaddara min na gaji mahaifi na a ranar Juma’a 23/08/2019.

ALBISHIR:- Allah ya taimake ka a iya saninka da mahaifinka, me za ka iya cewa, dangane da halayyarsa da salon shugabancin?

Mai Unguwar Munduba­wa:- A gaskiyar magana babu abin da zan fada game da shi wanda jama’ar Gezawa ba su san shi ba tunda shi dai mu­tum mai sassaukan ra’ayi da mutunta dan’Adam ga shi karamci da kuma jan mutane a jika.

Haka kuma kowa yasan halinsa kan talakawansa duk mai son ya ga fushinsa to ya taba talakansa, kuma shi sam ba ya riko ko kadan.

ALBISHIR: Ranka ya dade za mu so mu ji tarihin ka.

Mai Unguwar Mundu­bawa: Kamar yadda ka sani suna na Mahmud Aminu Yu­sufu an haife ni a Gezawa a shekarar 1975 a ranar 12 ga Disamba kuma na yi ma­karantar Firamare a Gezawa watau Gezawa Special ba ni da shekarun a kai na dai kuma na yi karamar Sakandare a nan Gezawa Yamma daga nan na koma FGC Kano, daga nan na koma Kano Cap­ital na kammala sakandare a Kano Capital, daga nan na tafi Jami’ar Maiduguri na yi Diploma a harkokin mulki (Public Administration) na koma na yi Digiri a Kimiyyar Siyasa (Political Science) daga nan kuma na kama aiki a a makarantar kudi ta Tarayya na yi hidimar kasa (NYSC) daga nan kuma suka rike ni daga baya na bari na tafi Fatakwal na kama aiki da wani kamfani INTENCE mai Martaba Sarki Ado Bayero ne shugaban kamfanin Oil & Serbices ne, na bari na koma hukumar NAPTIP, hukumar yaki da fataucin yara da bau­tar da su nan ma na bari zuwa dan lokaci.

Daga nan sai na dawo na fara aiki a nan jihar Kano a KNUPDA na koma ma’aikatar raya karkara na dan yi aiki kadan ban dade ba na shiga harkokin kasuw­anci.

Na yi kasuwanci iri da­ban-daban daga nan muka bude kamfani ko da yake ba mu ne asalin bude shi ba muna yin tuntubar hukumar harkar jiragen sama wadda suka shafi kayayyaki daga nan muka bude wani kam­fanin da muke harkar gine-gine da sauran aikace-aikace.

ALBISHIR:- Ranka ya dade ana cikin wannan al’umma kenan Allah ya kawo rasuwar Hakimi?

MAI UNGUWAR MUN­DUBAWA:- Haka ne, ina cikin wannan harka Allah ya kawo rasuwar mai gida, kuma Allah ya kaddara ni na gaje shi.

ALBISHIR:- Ranka ya dade a ranar da aka nada ka, al’ummar Gezawa sun fito kwansu da kwarkwatarsu da nuna maka goyon baya da murnar gidanku bai mutu ba, ya ya ka ji a ranka?

MAI UNGUWAR MUN­DUBAWA:- Gaskiya ba zan iya kwatanta farin ciki na ba, abin da kawai na dauka shi ne nuna kaunar mutanen Gezawa, haka su ma suke kauna ta.

Kasan babu mai dadi a rayuwa ka ji ashe wanda kake so shi ma yana son ka, ka ga a nan zama zai yi dadi kenan.

Kuma ina alfahari da al’ummar Gezawa kasance­warsu kishin zuci da neman na kai ba su da kasala da mutuwar zuciya fata na shi ne a shirya nake na hidimta wa jama’ata tare da kawo ci gaba cikin yardar Allah.

ALBSHIR:- Muna go­diya ranka ya dade.

MAI UNGUWAR MUN­DUBAWA:- Ni ma nagode kwarai.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: