Bunkasa ilimi tun daga tushe: Gwamnatin Ganduje ta cim ma nasara 

Bunkasa ilimi tun daga tushe: Gwamnatin Ganduje ta cim ma nasara 

Daga Jabiru Hassan 

 

Gwamnatin jihar Kano ta himmatu wajen gudanar da muhim­man ayyuka na raya kasa a birni da yankunan karkara, harkar bunkasa ilimi ma dai tana daga cikin fannonin da gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje yake bai wa kulawa ta musamman, tare da tabbatar da cewa, wan­nan fanni ya zamo ingantacce ganin yadda duniya take tafi­ya bisa sauyin zamani.

Ko a makon da ya gabata, gwamnatin Kano ta gudanar da wani muhimmin aiki na bai wa fannin ilimi kulawa ta musamman wajen bai wa kowace majalisar kara­mar hukuma tsabar kudi har Naira miliyan 20 domin yin gyare-gyare a makarantun da ke yankunan su wanda kuma hakan ya yi wa al’umar ji­har ta Kano dadi kwarai da gaske.

Wakilin Albishir ya yi wani zagaye inda ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi domin jin ta ba­kin su bisa wannan abin kirki da gwamnatin ta yi ganin cewa, ilimi shi ne gishirin zaman rayuwa ga dukkanin al’umma, tare da duba wad­Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Id­ris, na yadda ya rungumi wan­nan kungiya da hannu biyu tun daga lokacin da aka kafa ku giyar ya zuwa wannan lokaci, sai ya ce, ya na fatan sauran shugabannin za su rika koyi da maimartaba Sarkin Zazzau, na rungumar kungiyoyin addini da hannu biyu tare da saurar­onsu, a duk lokacin da bukatar haka ta taso wa kungiyoyin.

ansu daga cikin makarantun firamaren da suke da matsal­oli na gine-gine da wuraren zagaya wa.

A karamar hukumar Dawakin Tofa, Albishir ta sami zantawa da sakataren ilimin yankin Malam Ado Yahaya Kwa, wanda ya bayy­ana matukar jin dadinsa bisa babban tunanin da gwamna­tin Kano ta yi na samar da kudade ga majalisun kanan­an hukumomi domin gyaran makarantu kamar yadda aka gabatar ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce “ko shakka babu, gwamna ya yi abin da ake nema tun lokaci mai tsawo wajen bai wa fannin ilimi ku­lawa ta musamman a kuma daidai wannan lokaci da ake bukatar ganin wuraren koyar da karatu suna cikin yanayi mai kyau, sannan na hak­ikance cewa, ilimi zai samu ci gaba a jihar Kano saboda yadda gwamnatin take bayar da dukkan tallafin da ake bukata wajen kyautata yana­yin koyo da koyarwa”. Inji shi.

Shi ma a nasa tsokacin malam Kabiru Bala Kafin Maiyaki, jami’in Hulda da jama’a na kungiyar iyaye da malamai ta kafin maiyaki yace abin da gwamnatin Gan­duje yayi na baiwa kananan hukumomi kudi domin yin gyare-gyare a makarantun dake yankunan su abune da ya dace duba da yadda ake da lalatattun gine-gine da kuma guraren zagayawa a makaran­tun yankunan nasu.

Sannan ya nunar da cewa yanzu lokaci yayi da iyaye da masu rike da yadda zasu kasance cikin himma wajen taimakawa gwamnati wajen ganin ana cimma manufofi na bunkasa ilimi a fadin ji­har Kano musamman yadda gwamna Ganduje yake ci gaba da kyautata yanayi na guraren koyon karatun, tareda fatan cewa za’a hada hannu domin yin aiki tare.

Haka kuma Malam Dan­juma daga karamar hukumar Makoda, daya daga cikin iyay­en yara yace” ilimi dai shine ginshikin zaman rayuwa, don haka yana dakyau mu iyayen ‘ya’ya mu tsaya sosai wajen tabbatar da cewà yaran namu sun sami ingantaccen ilimi tun daga tushe duba da yadda gwamna Ganduje yake bullo da sahihan hanyoyi na inganta wannan fanni “.

Da yake bayani kan wan­nan tallafi na naira miliyan 20 da gwamnatin Kano ta baiwa majalisun kananan hukumomi kuwa, shugaban karamar hu­kumar Gwarzo Injiniya Bashir Abdullahi Kutama MNSE, yace “ a matsayin mu na wadanda aka baiwa wannan aiki, ZANU yi kokarin ganin cewa munyi amfani da wadan­nan kudade bisa makasudin bada su, sannan zamu hada hannu da dukkanin masu ruwa da tsaki wajen yin wadannan gyare-gyare kuma masu in­ganci”. Inji Shi.

Injiniya Bashir Abdul­lahi Kutama yayi amfani da wannan dama wajen godewa gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje sa­boda aikace-aikace da ya gu­danar a karamar hukumar Gwarzo kuma masu matukar amfani ga al’uma duk da halin da ake ciki na tattalin arziki gashi kuma kowane yanki suna da nasu bukatun ganin cewa jihar Kano yana da fadi da yawan al’uma.

Wani dalubi daga karamar hukumar Bichi Nura Aminu yace sunji dadi da jin cewa gwamna Ganduje ya baiwa kananan hukumomi kudi do­min yin gyare-gyare a maka­rantun su ta yadda idan aka koma karatu zasu sami ajuju­wan su cikin yanayi mai kyau domin kyautata koyo da koyar­wa kamar yadda suke gani a wasu jihohin, sannan yayi kira ga dalubai yan uwansa da su tsaya suyi karatu domin sun fahimci cewa gwamnati Gan­duje yana son su sami cikak­ken ilimi kuma mai albarka.

Kusan dukkanin makaran­tun da wakilin mu ya ziyarta suna da bukatar gyara wasu kuma suna da bukatar gu­raren zagayawa da ababen zama musamman a yankunan karkara, sannan akwai bu­katar ganin ana yawan san­ya idanu Kansu musamman lokutan aiki ta yadda za’a kwarara gwuwoyin malamai da kuma su kansu daluban.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: