A Zamfara: Za a yanke wa direbobi hukuncin kisa

A Zamfara: Za a yanke wa direbobi hukuncin kisa 

Shuaibu Ibrahim Gusau 

 

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Bello Moham­med (Matawallen Maradun) ta yi alkawarin sake bullo da manyan hukunce-hukuncen kisa a kan direbobi masu tukin ganganci.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne, a lokacin da ya jagoranci mambobin majalisar zartarwarsa da kuma shugabannin kungiyar BUA zuwa ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, kan mutuwar mu­tane 15 daga masarautar .

Matawalle wanda ya nuna al­hininsa kan mutuwar mutane 15 da suka rasa rayukansu, sakama­kon tukin ganganci da wani di­reban babbar mota ya yi a ranar Larabar da ta gabata a kan han­yar Gusau zuwa Funtua.

Bello ya sanar da gudum­mawar Naira miliyan 2 ga iyalan kowanne mamacin wanda ke da mata, sai Naira miliyan 1.5 ga iyalan wadanda ba su da aure a cikin su.

Gwamnan jihar Zamfara ya kara da cewa, zai sanya dangin kowane daga cikin wadanda abin ya shafa a kan alawus na Naira dubu 50 kowane, ya ce za su ci gaba da kasancewa a cikin jerin albashin jihar har zuwa karshen lokacin da ya ke gwamnan jihar.

Ya kara da cewa, gwamna­tinsa za ta gabatar da amfani da na’ura na auna saurin gudu, a kan manyan tituna da kuma auna nauyi a kan manyan motoci da kuma gwajin magunguna, a kan direbobi domin kaucewa tukin ganganci da rikon sakainar kashi wanda galibi kan jawo rasa rayu­kan mutane.

Matawalle ya ce, daukar matakan sun zama dole, saboda direbobi da danginsu ba za su kara tunanin za su samu sauki idan direbobin suka kashe wani, domin a cewarsa, rayukan ‘yan jihar sun fi kowane abu muhim­manci.

Ya bayyana hatsarin a matsa­yin babban abin tunawa tare da yin kira ga dangin mamatan da su dauki hakan a matsayin aikin Allah, yana mai addu’ar Allah ya karbi rayukan mamatan a sanya­su cikin Jannatul Firdaus.

Tun da farko, jagoran tawagar daga BUA, Injiniya Aminu Su­leiman ya ce, sun je jihar ne domin jajantawa gwamnati, ma­sarautar Gusau, mutanen jihar da dangin wadanda suka rasa rayu­kansu sakamakon hatsarin da ya rutsa da direban kamfanin.

Ya roki Allah da ya gafarta wa marigayin ya takaita abin da ya faru, kuma ya sa gwamnati da jama’ar jihar su yi farin ciki da wannan lamarin.

A nasa martanin, Mai marta­ba Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello ya gode wa gwamna Ma­tawalle da kamfanin BUA kan damuwar da suka nuna inda ya ce, kowace rai dole ne ta danda­na mutuwa kuma a matsayinmu na Musulmai, irin wadannan abubuwan ana yawan ganinsu a matsayin wani aiki na Allah, wanda ya fi kowa sanin dalilin da ya sa suke faruwa a lokacin da suke faruwa.

Basaraken ya bayar da tab­bacin cewa, za a yi amfani da gudummawar da gwamnan ya bayar sosai domin amfanin hakan.

Ziyarar ta’aziyyar ta samu halartar Sanata Sahabi Ya’u, Ka­kakin majalisar dokokin jihar, Alhaji Nasiru Muazu Magarya, SSG, Alhaji Bala Bello Maru, shugaban ma’aikata, Kanar Bala Mande (mai ritaya), shugaban ma’aikata, Alhaji Kabiru Balar­abe, kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, Ma­taimakin Shugaban Ma’aikata, Dokta Bashir Mohammed Maru da Babban Sakatare. Ofishin gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Jafaru Maradun da sauransu.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: