Sharudda 8 ga masu aikin Hajjin bana

Sharudda 8 ga masu aikin Hajjin bana 

Tare da Aliyu Umar 

 

A kalla mutane 10,000 ne za su yi aikin Hajji na bana saboda annobar Korona. Yayin da ya rage kasa da mako guda a fara gudanar da aikin Hajjin bana a kasa mai tsarki, hukumomin Saudiyya na ci gaba da shirye-shiryen aiwatar da muhimmiyar Ibadar a bana.

A bana dai mutane 10,000 ne kacal za su yi ibadar kuma mazauna Saudiyya kawai, ciki har da ‘yan kasar da kuma wadansu da suka je daga ketare. An rage yawan masu zuwa ibadar aikin Hajjin ne saboda Annobar Korona wadda ta addabi al’ummar duniya.

Tuni dai mahukunta a Saudiyya suka fitar da wadansu sharudda guda takwas ga Mahajjatan na bana, sharudan kuwa sun hada da: Dole ne duk wanda zai yi aikin Hajjin bana ya kasance ba shi da ciwon siga.

Dole mahajjata su kasance ba su da lalurar hawan jini. Dole mahajjata su kasance ba su da wata lalura da ta shafi zuciya. Dole mahajjata su kasance ba su da wani ciwo ko lalura da ta shafi numfashi. Ya kasance mahajjata ba su kamu da annobar Korona ba ko kuma sun yi a baya.

Shekarun mahajjaci dole su kasance tsakanin 20 zuwa 65. Dole mahajjata su kiyaye da dokokin da ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta gindaya domin kariya daga annobar Korona, ma’ana dole su kiyaye da dokar killace kai mako biyu kafin aikin Hajji da kuma mako biyu bayan kammala aikin Hajji.

Sannan ya kasance dukkanin Alhazai da Hajiyoyin bana ba su taba yin aikin Hajji ba. Karin bayani game da aikin Hajji: Aikin Hajji daya ne daga cikin shikashikan addinin Musulunci biyar, da aka wajabta wa Musulmai masu hali su yi ko da sau daya ne a rayuwarsu.

Ana gudanar da aikin Hajji ne a kwanaki biyar wanda ake farawa daga 8 ga watan Zul-Hajji zuwa 12 ko 13 ga watan. A duk shekara fiye da mutane miliyan biyu da rabi ne ke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya, wanda shi ne taro mafi girma a duniya.

Sai dai a bana annobar Korona ta sauya al’amura, har ta kai ga hukumomin Saudiyya sun sanya wadansu ka’idoji

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: