Rundunar SAHEL SANITY ta hallaka ‘yan bindiga

Rundunar SAHEL SANITY ta hallaka ‘yan bindiga 

Shu’aibu Ibrahim daga Gusau 

 

Dakarun sojojin Nijeriya da ke karkashin rundunar Operation SAHEL SANITY na ci gaba da yaki da ‘yan bindiga da masu satar shanu da garkuwa da mutane domin kokarin ganin an kawar da su daga Arewa maso yammacin kasar nan.

Mukaddashin jami’in yada labarai na rundunar tsaro ta kasa, Birgediya Benard Onkeuko ya bayyana haka a taron da ya yi da manema labarai a sansaninsu da ke Faskari cikin jihar Katsina.

Birgediya Benerd ya bayyana cewa, bayan samun bayanan sirri da dakarunsu suka yi, sun yi kokarin mamaye wata makaranta inda suka yi nasarar kama wani mai suna Musa Abubakar wanda aka fi sani da Buzu, mai safarar makamai ne kuma haifaffen kasar Nijar.

Sojojin sun kama Buzu tare da dan uwansa da ke gadi a makarantar, cikin binciken farko da suka yi masa ya nuna cewa, shi Buzu yana shigo da makamai daga Jamhuriyar Nijar, ta kananan hukumomin Sabon Birni da Isa da ke jihar Sokoto, a halin da ake cike yanzu haka Buzu yana hannun jami’an tsaro inda yake bayar da bayanai masu inganci.

A wani mai kama da wannan a ranar 25 ga watan Yuli na wannan shekara, jami’an tsaron da ke a Sabuwa sun sami labarin sirri na wadansu da suka yi garkuwa da mutane a garin inda suka bi sahu domin gano wadanda aka yi garkuwa da su, sai dai daga bisani, barayin mutanen sun tsere sun bar wadanda suka sato har mutum hudu, sojojin sun sami nasarar ceto mutanen, suka mayar da su gidajensu.

Ya kara da cewa, dakarun sun yi amfani da bayanan sirri suka afkawa wata maboyar ‘yan bindiga da ke Gurbin Baure, sun kuma sami nasarar hallaka mutane biyu daga cikin ‘yan bindigar da suka yi kokarin tserewa suka kuma kama mutane uku, haka kuma sojojin da ke kula da shiyyar Bena sun yi sintiri zuwa kauyukan Unguwar Yara da Bankami. da Faduwa da Danlayi duk a jihar Zamfara.

Haka kuma sojojin sun yi nasarar kama wani mai bai wa ‘yan bindiga bayanai mai suna Garba Faduwa, sun kuma yi nasarar ceto wani wanda ‘yan bindiga suke tsare da shi mai  suna Alhaji Lawal Mamman wanda yanzu haka yana nan yana karbar magani a Asibiti saboda rauni da ‘yan bindiga suka ji masa a lokacin da yake hannunsu.

Shugaban rundunar sojojin kasa na Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, a cikin sakonsa ga dakarun sojojin ya ce su kara zage damtse, ya kuma jinjina masu a kan nasarori da suke samu

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: