Rufe kan iyakoki: Amirka ta yi wa ‘yan Afirka korar kare

Rufe kan iyakoki: Amirka ta yi wa ‘yan Afirka korar kare 

Amirka ta mayar da ‘yan Afirka kusan 190 zuwa kasashensu na asali duk da dokar takaita tafiye-tafiye domin hana bazuwar annobar korona, matakin da masu rajin kare hakkin dan’adam ke kallo a matsayin wariyar launin fata. 

 

Amirka ta yi gaban kanta wajen tasa keyar ‘yan Afirka zuwa kasashensu na asali, inda ta yi biris da dokar hana tafiye-tafiye tsakanin kasa da kasa.

Wadansu alkaluma da hukumar shige da fice ta Amirka ta fitar, sun nuna cewa, daga ranar 1 ga Maris zuwa 20 ga Yunin bana, an kori ‘yan Afirka 189 a daidai lokacin da ake tsaka da fama da annobar korona.

Kasashen da Amirkar ta mayar da su kasashensu sun hada da Nijeriya da Gh

Kasashen in ban da Masar duk sun rufe kan iyakokinsu tun bayan barkewar korona a farkon wannan shekara, yayin da Amirkar ke amfani da jiragen haya wajen gwamutsa ‘yan Afirkan domin mayar da su nahiyarsu ta asali.

Salon da Amirkar ta yi amfani da shi, shi ne sanya ‘yan Afirkan a cikin jirgin fasinjan kasashe makwabta da ba su rufe iyakokinsu ba, inda daga nan bakin za su kama hanyar garuruwansu.

Kungiyar kare hakkin baki da hadin gwiwa tsakanin Kamaru da Amirka, ta yi tir da matakin tasa keyar ‘yan Afirkan, tana mai bayyana haka a matsayin nuna wariyar launin fata.

Matakin mayar da baki ‘yan Afirka gida, ya ta’azzara karkashin mulkin shugaba Donald Trump, inda gwamnatinsa ta takaita shigowar baki daga Nijeriya da Tanzania da Sudan da Eritrea da Libya da kuma Somaliya, matakin da masu rajin kare hakkin dan’adam suka yi tir da shi.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: