Masu maganin gargajiya, magori a yi sassauci

Masu maganin gargajiya, magori a yi sassauci 

Daga Salihu S. Gezawa 

 

An yi kira ga masu sanaar magungunan gargajiya da ke fadin kasar nan kan su yi sassauci da rangwame ga alumma masu neman magani da ke zuwa wajensu domin neman waraka.

Bayanin ya fito daga bakin babban jagoran kungiyar masu magungunan gargajiya na Nijeriya kuma magayakin Gezawa, Dokta Shuaibu Sale Damuna a zantawarsa da Albishir a gidansa da ke garin durumin Shura da ke karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Damuna ya ce a batu na gaskiya wajibi ne ya ja hankalin masu magungunan gargajiya musamman wadanda suke kara wa marar lafiya kudi idan ya zo neman magani inda sam hakan bai da ce ba domin ya yi wani irin tsari ba shi ne abin da ya kamata ba.

Dokta Damina ya ce tun da yake bayar da magunguna na cututtuka daban bai taba cewa, ga wani kudi mai nauyi da za a ba shi ba, zai duba marar lafiya bisa koyarwar addini da itatuwa kuma cikin yardar Allah a samu sauki.

Dokta Damina ya ce ganin irin gudunmawar da yake bayarwa da sadaukar da kai yasa mai girma Hakimin Gezawa Alhaji Muhammadu Aminu Yusufu mai unguwar Mundubawa (Marigayi) ya girmama shi da sarautar Magayakin Gezawa inda ya ce hakika wannan rawani ya kara masa kwarin gwiwa na taimakon alumma.

Daga nan sai ya yi kira ga alumma kan su rinka kula da lafiyar jikinsu, da tsabtar jiki da ta muhalli. Ya kuma kara jan hankalin alummar kasar nan kan bin dokokin mahukunta da masana harkar lafiya bias annobar Korona.

A karshe ya godewa gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, bisa tsayuwar daka da ya yi kan yaki da Annobar Korona da kuma bai wa harkar lafiya kulawa ta musamman kan harkar maganin gargajiya, ya godewa babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano da sarakunan Kano, Rano, Karaye, Gaya, da Bichi kan irin yadda suke ba shi babban jagoran masu magungunan gargajiya na kasa baki daya.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: