Kauran Bauchi ya zama Jagaban Katagum

Kauran Bauchi ya zama Jagaban Katagum 

Jamilu Barau daga Bauchi 

 

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed CON, (Kauran Bauchi) ya amintar da lakabin gargajiya na jagaban Katagum ta masarautar Katagum.

Da ya ke gabatar da wasikar neman mukamin ga gwamna a yau, a Gidan Gwamnatin Bauchi, Mai Martaba Sarkin Katagum, Alhaji Umar Farook ya ce, girmamawar ta kasance ne bisa girmamawa ga manyan ayyukan da gwamnan ya bayar wajen ciyar da masarautar.

Sarkin wanda ya yi magana ta bakin Makaman Katagum, Alhaji Aliyu Husaini ya ta ya gwamna Bala Mohammed murnar nada shi da ya yi.

Da yake mayar da martani, sabon jagaban Katagum, gwamna Bala Mohammed ya nuna godiyarsa ga masarautar bisa ga shi ya cancanci nadin.

Gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da dogaron amanar da aka nuna masa ta hanyar kokarin kare martaba da amincin masarautar Katagum ba kawai har da cibiyoyin gargajiya gaba daya.

“A madadin gwamnati da jama’ar jihar Bauchi, ya bayyana matukar farin cikin da kuka nuna ni da lakabin na gargajiya na Jagaban Katagum.

“A matsayina na memba na dangin Sarauta, gwamnati ta kudiri aniyar kare martabar sarakunan gargajiya a cikin jihar.”

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: