Kanawa sun yi na’am da gina hanyar jiragen kasa

Kanawa sun yi na’am da gina hanyar jiragen kasa 

Daga Jabiru Hassan 

 

Sakamakon yunkurin da gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke yi na bunkasa sufuri a jihar Kano, al’ummar jihar sun nuna goyon bayan su ga shirin gwamnati na samar da jiragen kasa wadanda za su yi aiki a cikin birnin Kano da kewaye ta yadda zirga-zirga zuwa wurare za ta zamo cikin sauki.

Wakilin Albishir ya yi wani zagaye na jin ra’ayin al’umma kan wannan batu na samar da jiragen kasa a cikin kwaryar birni da kewaye, inda dukkanin mutanen da aka tattauna da su suka bayyana amincewarsu da wannan ci gaba musamman ganin yadda zamani mai tafiya da sauye-sauye ta kowane fanni.

Malam Sagir Mohammed da ke Dawanau gari ya bayyana cewa, “ko shakka babu, gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi tunani mai kyau musamman ganin yadda harkar sufuri take kara bunkasa tattalin arziki da kuma ayyukan yi ga al’umma bisa la’akari da muhimmancin ta, domin haka mun goyi bayan wannan sabon ci gaba”. Inji shi.

Haka kuma wani mai sana’ar sayar da litattafai da ke Bata Coca-cola, Alhaji Murtala Adamu ya shaidawa Albishir cewa, gaskiya idan aka samar da jiragen kasa daga Dawanau zuwa Bata za a samu ci gaba sosai duba da yadda yanzu birnin Kano yake kara bunkasa da cushewa fiye da yadda yake a shekarun baya.

Bugu da kari, su ma mutanen da ke kan titin Zariya har zuwa kwanar Dawakin Kudu sun bayyana cewa, samar da jiragen kasa a birnin Kano da kewaye zai taimaka sosai wajen kawo saukin sufuri tare da kara samar da ayyukan yi ga al’umma da kuma bunkasa tattalin arziki cikin sauri.

Dukkanin mutanen da suka zanta da wakilinmu sun yi watsi da ‘yan adawa masu kushe wannan yunkuri da gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke yi na samar da jiragen kasa a cikin birnin Kano da kewaye domin bunkasa tattalin arziki da sufuri bisa la’akari da yadda Kano ke samun ci gaba ta kowane fanni na rayuwar al’umma.

Idan dai za a iya tunawa, gwamna Ganduje ya bukaci majalisar jihar Kano ta amince masa ya nemi izinin daga majalisar kasa domin ciyo bashin kudaden da za a yi amfani da su wajen gudanar da wadannan muhimman ayyukan na samar da jiragen kasa ba tare da tsaiko ba.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: