Kakaki UNIKUE ta karrama masu kishi a Katsina

Kakaki UNIQUE ta karrama masu kishi a Katsina 

Rabi’u Sanusi Daga Katsina 

 

An bukaci sauran al’umma musamman masu hannu da shuni da su yi koyi da irin halin Alhaji Shamsu Dahiru Ahmad Dandagoro wajen taimakon al’umma a jihar Katsina.

Bayanin hakan ya biyo bayan karamma wadansu daga cikin masu taimakon al’umma da kamfanin Kakaki Unikue Award ta shirya domin sakawa wadansu masu hidimtawa al’umma.

Haka zalika a jawabai daban-daban da aka gabatar yayin taron ya yi nuni da irin kokarin matashin kuma mai hidimtawa al’umma na daya daga cikin abin koyi ga sauran al’umma.

Sannan kuma da yawan wadanda aka karrama a ciki sun tabbatar da cewa, su ma ba yin su ba ne yin ubangiji ne. Shi ma da yake wa manema labarai karin bayani jim kadan bayan kammala taron, Alhaji Shamsu Dahiru Ahmad, ya nuna godiya ga Allah madaukakin sarki da ya sa ya zamo daya daga cikin wadanda aka karrama.

Alhaji Shamsu, ya bayyana cewa, gaskiya bai san za a karrama shi ba, kawai ya dai ji an kira shi a waya aka shaida masa cewa, za a karrama shi bisa kyautata wa al’umma da yake yi.

Irin ayyukan da Alhaji Shamsu Dahiru yake gabatarwa sun hada da taimakon marayu, taimaka wa gajiyayyu,  bayar da jari ga masu karamin karfi, da dai sauran su.

Haka kuma Shamsu Dahiru ya bukaci sauran matasa da su tashi tsaye wajen taimaka wa mabukata tare da gajiyayyu.

Alhaji Muhammadu Usman Sarki wanda yana daga cikin iyayen taro, ya kuma kara tabbatar da cewa, dukkan matasan da suka jajirce to lallai sai sun samu nasara a lamuran su.

Shi ma tsohon Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, kuma dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kusada, Kankia Alhaji Abubakar Yahaya Kusada, ya nuna godiya bisa wannan yunkuri na matasan na Kakaki.

Wadansu daga cikin wadanda aka karrama sun hada da Alhaji Shamsu Dahiru Ahmad, Abubakar Yahaya Kusada, Ibrahim Bashir mai Amana Design, Nasiru Abubakar Jalli sai MD na Kasaroma watau Injiniya Yazid Abukur.

Manyan baki sun hada da Alhaji Muhammadu Usman Sarki shugaban Kamfanin Al-dusar Group of Company, Sai Malam Salisu daga makarantar Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina.

Akwai kuma fitaccen danjarida Malam Danjuma Katsina tare da Dokta Sani Abdu Fari da dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Katsina, Alhaji Abu Ali Albaba da dai sauran su.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: