Gwamnatin Zamfara, a waiwayi hukumar sufuri

Gwamnatin Zamfara, a waiwayi hukumar sufuri 

Shu’aibu Ibrahim Daga Gusau 

 

An yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara, a karkashin jagorancin Bello Muhammad Matawalle, da ta waiwayi motocin sufuri na jihar (Zamfara State Transport Authority) a turance domin ceto rayukan al’ummar jihar.

 

Hakan ya fito daga bakin wani fasinja mai suna Abubakar Galadima da motar ta lalace yana ciki, a lokacin da yake kan hanyarsa zai shigo Gusau daga Abuja, a zantawarsa da wakilinmu bayan ya iso Gusau, ya kara da cewa, ya kamata gwamnati ta dubi wannan hukumar saboda ko ba komai gudun salwantar rayukan mutane.

Abubakar ya kara da cewa, duk motocin sun gaji wadansu daga cikinsu tun na lokacin tsohuwar gwamnatin Mamuda Aliyu Shinkafi ne, da na Shehi domin haka a cewarsa motocin sun dauki shekaru a kan hanya suna bugun ramuka, hakan yasa ya ce motocin ba sa zuwa nesa daga Kaduna sai Zariya.

Yin wannan korafin yasa wakilinmu ya ziyarci hukumar wadda ke karkashin Alhaji Aminu Garba (Papa) domin jin ta bakinsa, ya kuma bayyana cewa, lallai wadannan motocin sun yi shekaru goma zuwa tara, kuma zuwan wannan gwamnati sun rubata mata korafinsu, ya kara da cewa, sun kai korafin ga gwamnati ta amince kuma ta sayo motoci sai dai kawai ana jiran lokaci domin a bayar da su, ma’ana lokaci kawai ake jira.

Aminu ya bayyana cewa, babban abin da suke fama da shi yanzu shi ne yadda motocin suke yawan lalace wa domin a cewarsa ko cikin satin da ya gabata motocinsu guda shida suka buga a hanya.

Ya kara da cewa, idan ka duba kusan abin da motar za ta ajiye shi za ta cinye a wurin gyara, ya ce ga kuma sauki da jihar Zamfara ta yi wa fasinjoji, fiye da sauran jihohi.

Aminu ya ce babban abin da yake ci masu tuwo a kwarya shi ne rashin samun tasha ta su ta kansu a sauran jihoji, ya ce hakan yasa duk inda suka kai fasinja suka sauke zai yi wuya su sami lodi cikin lokaci sai sun kwana daya zuwa kwana biyu.

Shugaban ya kara da cewa, saboda rashin samun tasha ya sa ba sa zuwa jihar Katsina ba sa zuwa Bauchi ko Gombe, ya ce Sokoto ma da suke zuwa sun yi yarjejeniya ne da su duk lokacin da motar Zamfara ta je jihar to sai gobe ta yi lodi, ya ce hakan yasa dole motar ta kwana ko da ta zo da wuri.

Aminu Papa ya kara da cewa, a jihohin Kaduna da Abuja sun sami wuri ne suka kama haya, Kano ne kawai suka sami fahimtar juna suka shiga cikin tasha a Jan Bulo.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: