Daminar bana, taki ya yi tsada

Daminar bana, taki ya yi tsada 

Daga Alhassan Abba Yankatsari 

 

Malam Musa Abdullahi Zara ya bayyana cewa, taki bana ya yi tsada ba kamar bara ba kuma duk da haka ya kara da cewa, idan ka je wajen da za ka samu takin sai ka sha wahala saboda takin ya yi wuyar samu.

Sannan ya yi kira ga gwamnati da ta samar da taki a kan lokaci saboda idan gwamnati ta samar da taki a kan lokaci shi ne manomi zai samu damar ya saya a idan ta samar da shi.

Saboda idan gwamnati ba ta samar da taki da wuri ba to takin zai yi wuyar samu saboda ba ta samar da shi da wuri ba, to ka ga dole ya yi tsada a kasuwa.

Musa ya bayyana cewa, takin kala uku ne, akwai NPK ana sayar da shi a kan kudi Naira dubu biyar da dari biyar watau taki dan Buhari, sannan kuma Yuriya ana sayar da shi a kan kudi Naira dubu tara da dari biyar, gwaldin kuma ana sayar da shi a kan kudi Naira dubu goma sha shida.

Game da shi kuma kudin da za a sayi takin ya yi wuyar samu, saboda mun yi jiran tallafin gwamnatin tarayya wadda za ta tallafa da taki da kuma maganin feshi amma har yanzu bai fito ba.

Musa ya kara da cewa, akwai matsalar tsutsa da take damunsu, saboda matsalar tsutsa idan suka yi shukar wake sai tsutsar ta cinye waken to muna kira ga gwamnati da ta taimaka mana da maganin feshi wadda za mu fesa domin mu yi maganin wannan matsala da ta addabi shukar waken mu.

Sannan kuma Musa ya yi kira ga Ministan noma da albarkatun kasa Alhaji Sabo Nanono da ya taimaka da ya fito mana da tallafin taki da kuma maganin feshi.

Ya kara da cewa, shi karamin manomi shi ya kamata a taimaka wa da tallafin taki da wuri.

Musa ya yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta dinga bin sawun tallafin da ta kawo saboda idan aka bai wa wadansu tallafin sai su sayar da shi ba sa amfani da shi ta hanyar noma.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: