Cin zarafin Musulmi:Faransa ta nuna wa Sin yatsa

Cin zarafin Musulmi:Faransa ta nuna wa Sin yatsa 

 

Faransa ta bayar da shawarar aikawa da tawagar kasashen duniya karkashin jagorancin hukumar kare hakkin dan’adam ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin Dinjiang, da ke Arewa maso yammacin kasar Sin, domin gudanar da binciken halin da ‘yan tsirari musulmin ouïghoure ke ciki.

A lokacin da yake tsokaci kan halin da al’ummar musulmin da ake tsare da su a sansanonin yankin Ouïghours na kasar ta Sin ke ciki, Ministan harakokin wajen Faransa Jean Ybes Le Drian ya sanar da Majalisar Dokokin kasar ta Faransa cewa, a yankin ana aikata abin da ya saba wa tsarin da babbar yarjejeniyar duniya kan kare hakkin dan’adam ta tanada, inda Sin ke ci gaba da tsare musulmi a gidajen kurkuku da kuma hana su fita daga gidajensu, tilasta masu ayyukan karfi ko kuma hana su gudanar da wadansu fannoni n addininsu na musulunci.

Ko a makon da ya gabata a gaban Majalisar Dokokin ministan Le Drian ya bayyana abin da ke faruwa na cin mutuncin ‘yan tsirarun musulmi a yankin na kasar Sin da zama abin da duniya ba za ta taba amince da shi ba, inda ya bukaci aikawa da tawagar kasashen duniya mai cin gashin kanta a yankin na Dinjiang domin gudanar da bincike.

A lokacin da take mayar da martani kan furcin, na Farnsa kasar Sin ta bayyana zargin da zama na karya tsabagenta. Kakakin fadar gwamnatin Pekin ya ce, siyasar kasar a yankin Dinjiang ba ta takura wa al’ummar da ke rayuwa a yankin ba ce, inda ya ce, siyasar kasarsa a yankin ba ta take hakkin dan’adam ko takaita ‘yancin addini ba ce, amma tana yaki da ayyukan ta’addanci da kuma tayar da kayar bayan ‘yan aware a yankin.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: