Shugaban PTD ya ankarar da gwamnatoci kan aikace-aikacenta  

Shugaban PTD ya ankarar da gwamnatoci kan aikace-aikacenta  

Daga Shafiu Yahaya 

 

Kwamared Muhammad Sanin Malam Garba Shugaban kungiyar PTD na jihohin Arewa Maso Yamma wanda suka kunshi jihohi bakwai na Arewa da ofishinsa ya ke Kano, ya ankarar da gwamnatoci kan al’amuran kungiyar.

Ana yin sa ne domin jawo hankalin gwamnatin tarayya na ta gaggauta gyara manyan titi na guda uku da suka ta so daga inda ake dauko albarkatun man fetur a kudancin kasar nan zuwa Arewacin kasar nan wadanda su ne masu dakon albarkatun man su ke bi su kawo Arewa wanda dukkanin su sun lalace sun kuma zama tarkon mutuwa da samun raunika da hallakar dukiya ga ‘yan kungiyarmu ta PTD da su ke aikin na dakon albarkatun manfetur daga Kudu zuwa Arewacin.

Jawabin ya futo ne ta bakin shugaban PTD mai jihohi bakwai irin su, Kastina, Jigawa, Bauchi, Yobe,

Gombe, Zamfara, na Arewa Alhaji Muhammadu Sanin Malam Garba Lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ofishinsa kwana biyu da fara yunkurin ceto rayuka da dukiyoyin Al’umma a ranar Talata da ta gabata.

Alhaji Muhammadu Sani Malam Garba shugaban PTD ya ce, lalacewar hanyoyin irin su hanyar Makwa Benin zuwa Uweri, da hanyar Fatakol, hanyar Birnin Gwari, Bidda zuwa Suleja, da hanyoyin da ake bi a kawo mai Arewa duk sun lalace kowacce hanya in ka bi zaka ga Gosulo mai yawa Direbobi na shan wahala a hanyoyin ai kwana biyu, uku, biyar har zuwa sama da haka kafin direba ya kawo mai Arewa wanda kamar ba ta Birnin Gwari ba, ba ta biyuwa saboda matsalar ta in an bi yu kuma wannan matsala na haddasa sace mana direbobi raunata su wanda wadansu yanzu haka su na asibiti, har ma da rasa rayuka, kwace motoci a hannunsu da dai saurar matsaloli da suka dami kungiyar ta PTD wanda ke so hanyoyin kawo albarkatun mai Arewa wanda idan ba ai haka ba yadda damunar nan ta zo akwai yuwuwar Arewa a dai na kawo albarkatu manfetu da ake fuskanta a wannan lokaci damuna.

Har ila yau ya ce, wadansu matsalolin kuma shi ne, yadda jami’an tsaro su ke da Get-Get a hanyar ta yadda tanya zaka sami Get fiye da 30 kuma kowanne su na karbar kudi ko mai sai ka ba su kuma hakan ta kan kawo sanadin ka kawo mai a duba a ga bai ciki ba, kuma kai amana aka baka ko da galan daya aka karba a gurinka ai kaga matsalace da kai da aka baka amana ka kawo wadannan na daga cikin matsalolin da mu ke so gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo mana dauki da saurin matsalolin da suka addabi wannan kungiya ta PTD domin kada Arewa ta rasa samun albarka tun manfetur da mu ke dakonsa daga can. A karshe dai ya ce, bisa kyakkyawan za to da su ke wa Gwamnatin ta su ta Muhammadu Buhari sun abin ba zai gagara ba kamar yadda na ba ya suka gaza

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: