Sojojin Nijeriya, a sauya dabarun yaki –Zulum

Sojojin Nijeriya, a sauya dabarun yaki –Zulum 

Sani Gazas Chinade Daga Maiduguri  

 

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa, lallai Nijeriya na bukatar kara yawan dakarun tsaronta domin samun nasara a kan ‘yan ta’addar Boko Haram da aka yi tsawon lokaci ana fafatawa da su.

 

Gwamnan ya yi bayanin ne a yayin da wata tawaga daga majalisar Dattijai ta kai ziyara jihar domin yi wa al’umma jaje da ta’aziyyar hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa a garuruwa daban-daban a jihar.

Tawagar Sanatocin na karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi, tare da mai tsawatarwa, Sanata Orji Kalu, sun ziyarci birnin Maiduguri domin nuna alhininsu ga al’ummar jihar bisa ga yawaitar hare-haren baya-bayan nan da ke afkuwa a yankin.

Zulum ya shaida wa ’yan majalisun da suka ziyarci jihar, inda a ciki har da tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima, cewa, akwai karancin so

jojin da suke tunkarar fafatawar, sannan kuma wani muhimmin abu shi ne, muna son gwamnatin tarayya ta bi matakin shigar da hazikan matasanmu na ‘Cibilian JTF’ cikin rundunar sojojin Nijeriya tare da sauran bangarorin tsaro na kasar, wanda hakan zai taimaka wajen kawo karshen ayyukan ’yan ta’addar Boko Haram.

Har ila yau, gwamnan ya nemi ‘yan majalisar Dattawan da su duba al’amarin wajen cike gibin da ake da shi a yaki da matsalar tsaro a yankin da ma kasa baki daya.

A nasa jawabin, shugaban tawagar, Sanata Yahaya Abdullahi, ya ce zauren majalisar ya ce an damka wa kwamitin nasu alhakin kai ziyara zuwa jihar Borno tare da mika jajensu dangane da kashe-kashen da jihar ke fuskanta.

Shugaban tawagar ‘yan majalisar ya yaba da kokarin gwamna Zulum “wannan shi ne shugabanci abin koyi” wanda hakan ya taimaka wajen dawo da lamurra, in ji shi.

Sanata Abdullahi ya kara da cewa, zauren majalisar Dattijai, ya samu labari mara dadi, na hare-haren ‘yan kungiyar a yankunan Gubio da Monguno, wanda hakan ya jawo majalisar ta bukaci shugaban majalisar ya hadu da shugaban kasa domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalar tsaron.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: