Ko-in-kula, matsalar da ke addbar mata, birni da kauye

Ko-in-kula, matsalar da ke addbar mata, birni da kauye 

Daga Zainab Sani Kiru 

 

Assalamu Alaikum yau zan yi duba a kan halin ko in kula da matanmu na karkara ke fuskanta kama daga kan iyayensu har izuwa mazajen da suke aura.

Da farko za mu yi wani dan tsokaci, mata suna da wata bai wa wacce Allah ya yi masu lokacin da Allah ya rarraba aikace-aikacen gida sai ya dorawa maza ragamar gudanarwa ta ciyarwa, da shayarwa, da tufatarwa da kare hakkokinsu da sauransu.

Kuma hikima irin ta Allah sai ya bai wa mata hikimar sarrafa maza duk da dawainiyar da Allah ya dora masu, mutum ko sarki ne idan ya fito fada zai rinka zare idanuwa yana muzurai amma yana shiga gida zai fara ‘yar murya. Matan karkara na fuskantar kalubale da kuma halin ko in kula da suke fuskanta daga iyayensu zuwa mazajensu.

Tabbas rayuwar mace a karkara na cikin wani irin jarrabawar rayuwar aure, wacce ke hana ta samun cikar burin kowace mace, kaso 70 cikin 100 sun kasance cikin halin ka-ka ni-kayin rayuwa, inda suke gwagwarmayar neman abin da za su rufa wa kansu asiri su da iyalinsu saboda gazawar hakan da suka sa mu daga mazajensu da ma iyayensu maza sukan dauki tallah daga kauyukansu

 

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: