Gwamnan Bauchi ya yi wa manoman jihar kaimi

Gwamnan Bauchi ya yi wa manoman jihar kaimi

Sule Aliyu Daga Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, ya ce ya shirya tsaf a yi noma da shi a wannan damunar ta shekarar 2020 domin bunkasa jihar da abinci.

Ba wata togiya tsakani na da wani, zan dauki fartanya na tafi gona domin ni ba ma’abocin yawace-yawace ba ne, ko tunkaho da zuwa Abuja, saboda babu wani abu da zan dauka a birnin Abuja.

Ya kara da cewa, idanu na a bude suke kan lamura, kuma ni mazaunin Bauchi ne, abin alfahari ne a ce na zauna a garin Bauchi har na tsawon watanni uku, ba tare da na je ko’ina ba, ko wani wuri daga garin Bauchi ba.

Muhammad ya umarci dukkam masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa da su rungumi aikin noma gadan-gadan domin wanzar da juyin juya hali a wannan fanni na rayuwa.

Sanata Bala Muhammad ya bayar da umarnin a garin Bauchi a Kamfanin BASAC lokacin da yake kaddamar da kasuwar sayar da takinzamani na damunar bana domin wadatar da jihar da ma kasa baki daya.

Ya ce, domin zurfafa ayyukan, na umarci ma’aikatar aikin gona ta jihar ta tabbatar da cewa, dukkan ‘ya’yan majalisar gudanarwa ta jiha su koma gona domin noma abinci da kayayyakin masarufi.

Na sake jaddada cewa, lallai kowane mai rike da mukamin siyasa a wannan gwamnati ya noma a takaice hekta daya na gona, domin haka, gwamna ya yi kira ga daukacin ma’aikatan gwamnatin jihar da su yi koyi da irin dabi’arsa, yana mai nusar da ma’aikata da su himmatu wajen tafiyar da aikaceaikacen gwamnati, la’akari da nauye-nauyen da jama’a suka dora masu.

Bala ya shaidawa taron bikin kaddamar da kasuwar cinikin takin cewa, muna fadi-tashin ganin cewa, mun sauke nauye-nauyen da jama’ar jihar mu suka dora mana, ba tare da yin wasa da wannan nauyi ba.

Ya zama wajibi a gare mu, mu yi duba da idon basira, saboda gani ya kori ji, kuma daga na gaba ake gane zurfin ruwa.

Zan tanadi gona kazalika na san mataimaki na ma manomi ne, saboda shi yake rike da sarautar sarkin ayyuka a masarautar Bauchi, shi ma kamar Bako da Tukura ne, duk Umbutawa ne”, Inji gwamna.

Daga nan, sai gwamna ya yi alkawari na dubawa da tabbatar da an bi wannan umarni na sa na jama’a su koma gona, yana mai cewa, matukar mun nuna misali, sauran manoma za su yi koyi, wanda zai sanya daukacin al’umma su goya baya.

Gwamna Bala, wandaya yi tir da halayyar wadansu mutane a baya, inda ya kasance taki da aka yi nufin jama’ar Bauchi da shi ake karkatar da shi zuwa kasuwa saboda son zuciya, sai ya yi gargadi da cewa, gwamnatinsa ba za ta lamunci ire-iren wadannan halaya ba. Ya ce, halayen mu kusan guda ne, kuma duk mun amince da hakan, kuma wadannan halaye ba su wuce na tabbatar da cewa, mun yi noma, kuma mun tabbatar da cewa, wadansu sun yi koyi da mu wajen ayyukan noma”.

Ya bayyana cewa, ana ta bibiyar tsare-tsaren ayyukan gona da ake dauke da su, domin ganin cewa, manoma sun juya akalar sana’ar ta su zuwa ta kasuwanci da za ta samar da abin hannu. Bala ya ce, ziyara da ya kai kasar Jamus a kwanakin baya, ta ba shi nasarar tattaro masu zuwa zuba jari ga jihar ta Bauchi, yana mai cewa, akwai kwarin gwiwa na kamfanoni da yawa da za su zuba jarinsu a bangaren noma a Bauchi da zummar kambama tattalin jama’a fiye da yadda man fetur zai yi.

Sanata Bala Muhammad ya sanar da cewa, gwamnati za ta sayar da buhun takin NPK kan kudi Naira dubu 5,000, kazalika buhun takin UREA, Naira dubu 7,000 ba kamar yadda ake sayar da shi a kasuwa ba na kudi Naira dubu takwas 8,000.

Daga cikin abubuwan da suka wakana a wajen bikin sun hada da baje kolin kayayyakin noma da kiwo da jihar ke sarrafa wa, Sanata Bala ya ce zai dauki mataki a kan wanda duk doka ta sa mu yana sayar da takin zamanin a kan kudi fiye da farashin gwamnati.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: