Faransa za ta jagoranci yakar ta’addanci -Tare da kasashen Sahel

Faransa za ta jagoranci yakar ta’addanci -Tare da kasashen Sahel 

Shugabannin kasashen G5 ko Sahel da na Faransa sun amince da shirin karfafa yakin da suke da ‘yan ta’adda a yankin Sahel bayan wani taro da ya yi nazari kan yadda yakin ke gudana da aka yi a kasar Mauritania.

Yayin taron a Nouakchott ta kasar Maurtania shugabannin kasashen da ke kawancen yaki da ta’addanci a Sahel sun yi bitar nasarori da kuma kalubalen da suke fuskanta tun bayan sabunta salon yaki da masu ikirarin jihadin da suka yi a watan Janairun da ya gabata.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, babban makasudin taron na baya-bayan nan shi ne, tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu a baya da kuma gyara kura-kuran da aka samu, game da daukar sababbin matakan da bai yi karin haske a kansu ba.

Sai dai daya daga cikin batutuwan da taron ya mayar da hankali shi ne, tsaurara sa ido kan iyakokin da suka hada kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar inda hare-haren ta’addancin suka fi kamari.

Yayin jawabi a taron, mai masaukin baki shugaban kasar Mauritania Muhammad Ould Shiekh Ghazouani ya ce, ba shakka sun sami nasarori da dama kan mayakan na ‘yan ta’adda, sai dai sun gaza shawo kan tarin kalubalen da har yanzu suke fuskanta, la’akari da yadda akidar ta’addancin ke dada bazuwa a sassan yankin Sahel cikin sauri.

Yanzu haka dai Faransa mai kimanin dakaru dubu biyar da ke jagorantar rundunonin kasashen G5 Sahel wajen yaki da ‘yan ta’adda a yankin, ta kara azama wajen kawo karshen mayakan da Abu Walid al-saharawi ke jagoranta, wadanda suka yi wa IS mubaya’a.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: