A Gombe: ‘Yan-sanda, maharba, sun kashe mai garkuwa, sun kama 1

A Gombe: ‘Yan-sanda, maharba, sun kashe mai garkuwa, sun kama 1 

Daga Danjuma Labiru Bolari, Gombe

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe da taimakon kungiyar kwararrun maharban jihar sun yi nasarar kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutane da suka sace wani magidanci mai suna Musa Rifa’i, suka kuma kama daya daga cikin 6 da suka shiga gidan Musa Rufa’i, a kauyen Yelwan Kashere a garin Pindiga yankin karamar hukumar Akko.

A lokacin da yake gurfanar da gawar wanda ‘yan sanda da maharban suka kashe da kuma wanda suka kama mai suna Babangida Musa, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe, Mai Kudi Ahmed Shehu ya ce, ‘yan sandan SARS, da taimakon maharban ne suka samu nasarar a lokacin da suka samu kiran gaggawa daga DPO na garin Kashere kan cewa, maharan sun shiga garin.

Kwamishinan ‘yan-sanda Shehu ya ce, masu garkuwa da mutanen sun shiga kauyen ne cikin dare inda suka shiga gidan wani mutum mai suna Malam Kawu Amada suka dake shi suka ji masa rauni kafin su ce masa ya kai su gidan Musa Rufa’i.

Ya ce, da suka sace Musa suna tafiya da shi wani waje ne da ba’a san ina ne ba suka ci karo da jami’an sa suka fara musayar wuta inda Musa Rifa’i, ya tsira suka kashe daya suka kama daya da rai sauran suka tsere da raunin bindiga Kwamoshinan ‘yan-sandan ya kuma ce, sun samu karamar bindiga kirar hannu a wajen wanda aka kama da babur Bajaj guda biyu ya kuma ce suna nan suna ci gaba da gudanar da bincike akai.

Da wakilin mu yake tambayar wanda aka kama Babangida Musa, ya ce, wani mai suna Ilu ne a garin Gobirawa ya tura su suje gidan Musa su karbi kudi a wajen sa domin yana da su kuma su kudin suke so.

Shi ma Musa Rufa’i, wanda ‘yan bindigar suka sace ya ce, yana kwance cikin dare sai ya ji mutanen sun shigo gidan sa ta gidan makwabcinsa, Malam Kawu Amada matar sa ta yi ihu sai ‘yan uwa suka fito da suka ga barayi ne, sai ya ce kar su taba su domin za su iya kashe su, a nan ne mutanen suka tafi da shi suna tafiya da suka sha wata kwana sai ya tsere ya fada wani gida suka kasa kama shi a haka ya kubuta

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: