Tunawa da Janar Abacha: Shekaru 20 baya

Tunawa da Janar Abacha: Shekaru 20 baya

Daga Ibrahim Abdu Zango

 

 Ya zame mana tilas mu tuna manyan kwarai wadanda suka yi wa Nijeriya hidima wacce har ta kai da rasa rayukansu.

Gaskiya dole a dauko tarihi tun wancan lokaci watau lokacin can-can baya, watau daga shekarar 1960-1966, shekaru shida managarta a zuciyoyin jama’ar kirki ba wai na kaza da kato ba, kasan a kan ce kaza ci-ki goge bakinki-ha, haka nema na tun da haka Allah ya halicce ta, kuma yau dan’adam sun zama kamar haka domin mance alherin da suka samu lokacin wadancan gwamnatoci, watau na shekarar 1960-1966 shekaru shida kacal amma masu gani sun gani ire-iren ayyukan kirkin da aka yi wadanda suka shafi kowa da kowa kamar harkar ilimi, tufafi, noma da dukkan ababen alheri, duk mun gani kuma daga karshe ‘yan siyasar Nijeriya a Kudu maso Gabas da na Yamma suka hada kai aka ture wannan gwamnati wadda ta yi iya kokarinta domin kyautata wa ‘yan Nijeriya.

Abin mamaki shi ne cewa, a lokacin kowace kusurwar Nijeriya akwai Firimiya na ta, watau Arewa akwai Sir, Ahmadu Bello, Yamma akwai Obafemi Awolowo, can kuma Kudu ta Gabas akwai Michael Okpara, bayan Zik shi ne shugaban kasa, sannan Sir, Abubakar Tafawa Balewa shi ne Prime Minister, ka ga ai Nijeriya ta sami zama cikin kwanciyar hankali a siyasance amma ina ‘yan ta kife cikin Kudu ta Gabas suka yi sharri irin na su aka yi yadda aka yi aka ture ko tumbuke rahamar da Allah ta’ala ya yi wa Nijeriya domin ta kasance babbar kasa a duniya.

To wannan ita ce barna ta farko wacce ta abkawa Nijeriya har yau din nan da ba a sami zaman lafiya ba cikin wannan makekiyar kasa a Afirka. To, ganin irin barnar ne ya kawo ire-iren su Janar Sani Abacha domin samun gyara mutocin Nijeriya wanda waccan barna suka kawo.

Janar Sani Abacha ya shigo mulki cikin matsanancin hali domin rikicin June 12, ya yikamari ainun domin mun san cewa, Yarawaba su ne ba sa son Abiola kususan manyansu amma da Janar Babangida ya tsokano tsuliyar dodo sai kawai Yarabawa irin su Tinubu, Wole Soyinka suka tayar da kayar baya aka yi ta fitintinu iri-iri har Janar Babangida ya gudu ya bai wa wani Bayarabe Mr. Shonekan shi ma suka ce da wa Allah ya gama su, suka fatattake shi shi ne dalilin shigowar Janar Sani Abacha mulkin Nijeriya.

Yarabawa a Nijeriya su ne matsalar Nijeriya amma wani katon dan Arewa wai shi Mathew Hassan Kukah yake dorawa ‘yan Arewa, domin kawai ba ta faranta wa ‘yan uwansa na Kudu. Shi Mathew Hassan Kukah wai shi Rabaran amma son zuciyarsa sai ya mayar da shi tamkar bai san komai ba.

To Janar Sani Abacha dai yanzu ya kai shekaru ashirin da biyu cikin kabarinsa kuma ya bar makiya cikin doron kasa kafin ta su mutuwar ta zo wacce ba su san yadda za ta zo masu ba, illa kawai mu mun san duk rai za ta dandani mutuwa saboda haka sai fatan alheri ga kowa da kowa domin komai nisan jifa Hausawa sun ce ‘zai dawo kasa’, ko me mutum ya yi akwai ranar sakamako ko yana so ko yana ki sai ta faru.

Janar Sani Abacha ya yi kokari irin na sa kuma makiya suna ta bibiyarsa domin a kama shi da laifin da su masu rai a yanzu sun tabka barnaku amma su ne suke zarginsa bayan baya nan a nan duniya, sun ga ta sa sai kuma wadansu su ga na su.

Naku, Kwamare Ibrahim Abdu Zango Kano, Nigeria– 08175472298

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: