Shekarar Buni daya ta fi shekaru 20 albarka -A Damagun

Shekarar Buni daya ta fi shekaru 20 albarka -A Damagun 

Yusuf Tata Daga Damaturu

A shekara daya na mulkin Mai Mala Buni mun samu abubuwan da a shekaru fiye da ashirin ba mu samu ba a Damagum.

Mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC ta jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Daushe Damagum, ya bayyana haka a wata hira da Jaridar Albishir a Damagum inda ya ce Damagum fadar mulkin karamar hukumar Fune ce kuma nan ne sarkin Fune yake da zama, amma shekara da shekaru mun nemi hanyoyin cikin gari ba mu samu ba sai bana inda aka yi wa hanya mai tsawon kilomita shida.

Alhaji Ibrahim Daushe ya ce, yaran mu fiye da goma sha biyar suna zaman jiran tafiya kasashen Turai domin karo ilimi wanda gwamnatin Mai Mala Buni ta dauki nauyin tura daliban Turai musamman yaran talakawan jihar.

Mu shugabannin Jam`iyyar APC tun daga matakin mazaba, har zuwa jiha muna samun kulawa daga gwamnatin jihar, haka lokacin rabon kayan tallafi wanda gwamnatin jihar ta bayar ya isa dukkan lungu wanda kusan kowane magidanci ya samu tallafi na zaman kulle da aka yi watannin baya.

Makarantun firamare da ke yankin karamar hukumar Fune sun samu kayan karatu da suka hada da tebura da bencina, Allon karatun azuzuwa da sauransu wanda kudinsu ya kai kimanin Naira miliyan arba’in da tara (N49,000,000.00) wanda ina daga cikin mutanen da suka rarraba wadannan kayayyakin a makarantun.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: