Samar da kudi bai-daya: Kasashen Faranshi sun ja kafa –Buhari

Samar da kudi bai-daya: Kasashen Faranshi sun ja kafa –Buhari  

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadi da matakin kasashen renon Faransa na janyewa daga shirin samar da kudin bai daya tsakanin kasashen yammacin Afirka, mai lakabi da ECO, yayin da ya gargadi takwarorinsa kasashen da ke cikin tattaunawar kaddamar da kudin kan su tashi tsaye wajen cika sharuddan da aka gindaya domin samun nasarar shirin.

Cikin sakon da shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce, abin takaici ne yadda kasashen su ma suka kirkiri nasu kudin bisa jagorancin Faransa wanda suka sanya wa suna kwatankwacin na kasashen yammacin Afirka, watau ECO.

Shugaban na Nijeriya ya ce, za a iya bayyana matakin kasashen renon Faransa da rashin mutunta tattaunawar da kasashen ke tsaka da yi game da batun samar da kudin bai-dayan, la’akari da yadda suka dauki wancan mataki na janyewa ba kuma tare da sanar da kowa a hukumance ba.

Ranar 20 ga Mayun 2019, Faransa ta aminta da janye takardar kudin CFA da take samar wa kasashen mallakinta domin hada-hada inda ta bayar da damar samar da sabuwar takardar kudin da ta yi wa suna ECO, kuma kasashen suka aminta duk da cewa, akwai waccan tattaunawa tsakaninsu da takwarorinsu na Afirka.

Buhari ya kuma jaddada matsayin Nijeriya na aiwatar da kudin, inda ya bukaci kowacce kasa da ta cika sharuddan da aka gindaya.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: