Mamakon ruwan sama ya wargaza gidaje a Damaturu

Mamakon ruwan sama ya wargaza gidaje a Damaturu 

Sani Gazas Chinade Daga Damaturu 

Ruwan sama da iska mai karfin gaske da Allah SWT ya saukar a garin Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe a farkon wannan makon da muke ciki sun yi sanadiyyar rasa rai da jin munanan raunuka tare da rushewar gidaje masu tarin yawa.

Kamar yadda lamarin yake wannan ruwan sama mai dauke da iska mai karfin gaske an fara shi da misalin karfe 8:30 na yammacin ranar Litinin, kuma farin farko iskar ne ta fara sauka, aka shafe akalla mintuna goma ana yin ta wadda a cikin mintunan da ba su wuce goma ba ne aka samu mafi yawan wannan barna ta rushewar gidaje da bishiyoyi masu tarin yawa kai kace ai iskar Tsunami ne ta abkawa wani yanki na garin Damaturu daga bisani ne kuma aka tsinke da ruwan saman da aka shafe kusan awanni biyu ana sheka shi kamar da bakin kwarya.

Wadansu unguwannin da wannan ibtila’in yafi afkawa sun hada da unguwar Nainawa, Fawari, Ajari Hausari, Kandahar Sabuwar Kasuwa, Pomfamari da Bindigari.

Wani mazaunin unguwar Nainawa da ibtila’i ta rutsa da gidansa Malam Kamilu cewa, ya yi idan ba mamaki da ikon Allah ba, da dai ace wannan iska da ruwa da ban mamaki kasancewar a kasa da mintuna kimanin goma aka yi iska amma kuma ta’adinta na da ban mamaki, domin kamar almara a cikin kiftawa sai kawai ya ga rufin kan dakunan sai an yi sama da su sai ga su a filin Allah.

Domin haka ya roki gwamnatin jihar Yobe da ta gaggauta kawo masu dauki, domin samun yadda za su shimfida hakarkarunsu.

Har zuwa ga hada wannan rahoto dai ba a kai ga kammala hada alkaluman adadin gidajen da suka salwanta sanadiyyar ibtila’i na ruwan sama da iska.

Wata majiya ta yi nuni da cewa, wannan barnar ruwan sama da iska wadansu kananan hukumomin jihar da suka hada da karamar hukumar Tarmuwa, Bursari, Bade da Nguru su ma sun yi fama da hakan wadda rahoton ke nuna cewa, akalla mutane kimanin 7 ne suka rasa rayukansu a rahoton da ba na hukuma ba. Tuni dai gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya umarci hukumar kai daukin gaggawa a jihar SEMA da ta kai daukin gaggawa ga al’ummomin da wannan ibtila’i ya afkawa.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: