Kungiyar rajin hada kan kasa ta karrama Ahmad Garzali

Kungiyar rajin hada kan kasa ta karrama Ahmad Garzali 

Kungiyar rajin hada kan kasa (Campaign for National unity debelopment association) ta karrama Ahmad Garzali tare da bashi lambar girmamawa a ranar Litinin da ta gabata. 

Lokacin taron sakataren kungiyar, Alhaji Abubakar Muhammad fara da cewa, kungiyar su ba ta siyasa ba ce, kungiya ce da take fada tallafi da taimaka wa ga mabukata tare da bada lambar girmamawa ga mutane masu taimakon al’umma a jihar Kano da kasa baki daya.

Sakatare ya kara da cewa, idan muka lura za mu ga cewa, bangaren kudancin kasar nan ya yi mana nisa ta wannan bangaren kungiyoyi masu bada tallafi da taimako, wannan dalilin shi yasa muka ga ya dace mu rika bada lambar girmamawa tare da karrama mutanen da suke bada tallafi ga al’umma domin mu kara musu kwarin kwiwa tare da zaburar da wadanda basayi domin su ma su fara.

Sakatare ya ce, a gaskiya kungiyar mu duk shekara take yin abin alkhairi na bada lambar yabo tare da karrama wa ga mutanen da suka cancanta a cikin jihar Kano, wanda hakan shi yasa muka zabi Alhaji Ahmad Garzali Inuwa Fagge bisa ga yadda muke samun labarin yadda ya ke taimakon al’umma ta bangarori da dama da suka hada da ilimi, lafiya da sauransu a fadin jihar, mun ba shi lambar girmama wa ne domin kara masa kwarin gwiwa wajen ci gaba da ayyukan da yake yi, tare da kiransa da ya dada kara fadada taimakonsa zuwa sauran kauyuka da suke a fadin jihar.

Da yake karda masa shaidar girmawar a madadinsa, Alhaji Muktar Gambo cewa ya yi, a gaskiya mun ji dadi sosai a matsayin mu na yan’uwa kuma aminai gare shi, domin ni kusan kwana biyu yana yi min waya yana gayamin cewa, ga wata kungiya za ta karrama shi, amma ba zai samu damar zuwa ba, sakamakon yana Abuja ga kuma yanayi da ake na annobar korona saboda na ce na wakilce shi.

A gaskiya Alhaji Ahmad Garzali Inuwa Fagge ba dan siyasa ba ne, domin ko ‘yan siyasa da dama sun nemi ya shiga harkar ta siyasa amma ya nuna masu ba shi da ra’ayi shi kawai mutum ne wanda ba shi da burin da ya wuce ya taimaki al’umma da dukiyar da Allah ya ba shi ta kowanne bangaren rayuwarsu.

 

saboda haka a madadin ‘yan’uwa da abokan arziki muna karba masa wannan lamba ta girmamawa tare da baka tabbacin cewa, insha Allah zai ci gaba da yin duk abinda ya da ce wajen taimakon al’umma kamar yadda ya saba, tare da aiki da kungiyar ku insha Allah, ya gode ya gode sosai.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: