A bana: Mahajjata dubu za su sauke farali -Saboda korona

A bana: Mahajjata dubu za su sauke farali -Saboda korona 

Gwamnatin kasar Makka ta ce, kimanin mutane dubu daya kacal da ke zaune a cikin kasar za su gudanar da aikin hajjin bana saboda annobar korona da ta tilasta rage yawan maniyyata.

Ministan kula da Aikin Hajji na kasar, Mohammad Benten ya sanar da haka ga manema labarai a birni Riyadh, yana mai cewa, adadin ma hajjatan na bana ka iya yin kasa da dubu daya.

Wannan na zuwa ne kwana guda da gwamnatin kasar ta bayar da tabbacin cewa, za a gudanar da aikin hajjin bana, amma ga mutanen da ke zaune a cikin kasar, ma’ana dai, ban da baki daga kasashen ketare. Tuni Musulmi daga sassan duniya suka fara mayar da martani, inda wadansu ke bayyana rashin jin dadinsu da matakin hana dimbin Musulmai sauke farali a bana.

A kowacce shekara dai, ana samun akalla Musulmai miliyan biyu da ke gudanar da aikin hajji a kasar Saudiya.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: