Zaman lafiya muke bukata, ba bikin cika shekara daya ba -Ibrahim Umar Gado Sony

Zaman lafiya muke bukata, ba bikin cika shekara daya ba -Ibrahim Umar Gado Sony

Shu’aibu Ibrahim daga Gusau 

 

Daya daga cikin jigajigan jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Umar (Gado Sony) ya bayyana cewa, al’ummar Zamfara zaman lafiya suke bukata ba bikin cika shekara guda kan mulki ba.

Umar ya bayyana hakan a lokacin da ya yi hira da wakilinmu a garin Gusau, ya kara da cewa, a wannan lokaci ba bikin cika shekara suke bukata ba domin a cewarsa gwamnatin Matawalle ta gama masu komai saboda cikin kwana dari Bello Matawalle ya dakatar da kashe mutane da satar shanu ta hanyar sulhu.

Ya kara da cewa, a shekara ta 2019 mutanen yankin birnin Magaji sun san halin da suke ciki kan matsalar tsaro, domin a cewarsa sai da kauyuka talatin suka zama kufai babu kowa duk sun watse.

Ibrahim ya kara da cewa, cikin wata uku da hawan gwamna Bello ya dauki matasa aiki ya bai wa mata tallafin kudi ga masu kananan sana’oi na dubu ashirin ga mata dari daga kowace karamar hukuma, ya kuma dauki matasa dubu shida da dari takwas yana ba su tallafi duk wata na dubu goma.

Dattijon ya ce cikin shekara daya gwamnan jihar Zamfara ya daidaita tsakanin al’ummar jihar musamman tsakanin ‘yan siyasa har ya kai wadansu suna barin jam’iyyunsu suna dawowa jam’iyarsa ta PDP kuma ana tafiya tare babu wata matsala.

Ya kara da cewa, duk da halin da kasarmu ta shiga ciki na COBID 19 bai hana gwamna gudanar da abin da ya kamata na ci gaban al’umma ba, kuma ya ce kowa ya ga yadda jihohi suka shiga takura amma jihar Zamfara haka suka zauna cikin walwala da aminci.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: