‘Ya’yan jam’iyar PDP a kara hakuri -S.A Ibrahim Ma’aji

‘Ya’yan jam’iyar PDP a kara hakuri -S.A Ibrahim Ma’aji

Mai bai wa gwamnan jihar Zamfara shawara kan harkar gamayyar jam’iyyu da kyautata hulda a jihar Zamfara, Ibrahim Ma’aji Gusau ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar PDP da su kara hakuri, domin a cewarsa a hankali gwamnati take tafiya.

Ibrahim ya bayyana hakan a lokacin da suke zantawa da wakilinmu da ke Gusau a ofishinsa, ya kara da cewa, ba lokaci guda gwamnati za ta bai wa kowa mukami ba, ya ce sannu a hankali ake bi, idan aka kara hakuri a cewarsa aka kuma sanya tawakkali to babu mai cin rabon wani, kowa rabon shi yake ci.

Mai bai wa gwamnan shawara ya ce domin a kawo kowa a tafi da shi yasa Bello Matawalle ya kira mutane musamman masu kananan jam’iyyu domin a tafi tare domin ciyar da jihar gaba.

Ya kara da cewa, akwai da dama cikin kananan jam’iyyu wadanda suka yarda a tafi tare da su, kamar jam’iyyar APP da ANPP da ACCORD da dai sauransu, wadanda a cikinsu gwamna ya bai wa wadansu mukamai na gwamnati. Ibrahim ya yi karin haske kan batun da wadansu suke yi na cewa, a daina karbar masu sauya sheka zuwa PDP, ya ce wannan ba daidai ba ne domin a cewarsa babu yadda za a yi dan siyasa ya ce ba ya son jama’a.

Ya kara da cewa, komai yawan jama’a babu wanda ba ya son kari, misali idan aka ce ku tara ne to za ku so ku zama goma ko fiye da haka.

Ya ci gaba da cewa, kada al’ummar jihar su manta cewa, lokacin da wannan gwamnati ta zo ta gaji matsaloli dabandaban, kamar matsalar tsaro da bashi da rashin kudi a aljihun gwamnati da dai sauransu, amma ya ce bai hana gwamna ya yi abin da ya kamata ba ga al’ummar jihar.

Saboda yana gudun kada jama’a su shiga wani hali, da kuma gudun kada a shiga harkar ta’addanci yasa gwamna ya samar da abubuwan yi na ci gaba, kamar tallafin mata na dubu ashirin da tallafin samar da abinci da kuma kawo matasa a ba su tallafin dubu goma duk wata da dai sauransu.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: