Sanata Gobir ya yi tir da hare-haren ‘yan ta’adda

Sanata Gobir ya yi tir da hare-haren ‘yan ta’adda 

Lemu Daga Sakkwato 

Sanata Ibrahim Abdulahi Gobir, Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Gabas a majalisar tarayya ya yi Allah wadai da maharan nan watau ‘yan ta’adda da suka kai hari a wadansu kauyuka na mazabarsa a inda suka kashe mutane da ba su ji ba ba su gani ba.

A yayin da yake zantawa da wakilinmu a Sakkwato a karshen makon da ya gabata ya ce harin ya yi sanadiyyar kashe mutane fiye da 70 a kauyukan Kusama da Aduwa da Gangara da ‘Yar bulutu da Garki da kauyan Kuzafa duka da ke cikin karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar. Sanata Gobir ya ce ta’adin da ‘yan ta’addan ke tabkawa a wadannan garuruwa ya yi muni domin kuwa a kullum wadannan azzalumai na cin karen su babu babbaka a inda suka kasance dabbobi marasa imani.

Ya ce wadannan mutane masu kama da dabbobi duk sun gurgunta albarkatun tattalin arzikin kasa a wadannan yankuna da jihar Sakkwato gaba daya. Ibrahim Abdullahi Gobir ya tabbatar cewa, zai yi amfani da kujerarsa domin samo mafita domin kakkabe wadannan azzalumai marasa kishi domin ganin gwamnatin tarayya ta shigo da karfinta wajen murkushe azzalumai.

A nan sai Sanata Gobir ya jinjina wa jami’an tsaro ganin yadda suka gaggauta shawo kan ta’addancin a wadannan garuruwa kuma akwai bukatar hada kai da sojoji domin gaggauta murkushe su domin dawo da zaman lafiya a jihar da kasar nan gaba daya.

Gobir ya ce ya dace sojoji su hada kaimi da sauran jami’an tsaro su kai farmaki cikin dazuzzukan yankin da aka yi wa lakabi da taken aiki da cikawa watau ‘operation idon mikiya’ domin murkushe azzalumai.

Sanata Gobir ya ce mayakan sama su kai farmaki suna jefa bamabamai su kuma sojojin kasa su bi kowane lungu da sako cikin dazuzzukan domin murkushe su.

Gobir ya yi amfani da wannan damar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da manyan makamai ga sojojin kasar nan domin samun karfin tunkarar ‘yan ta’addan gaba da gaba ya ce hakan ya zama wajibi ganin cewa, ‘yan ta’addan na rike da manyan makamai fiye da sojojin kasar nan.

Daga karshe Gobir ya bayyana cewa, babu wata gwamnatin da ta taba kasafta dimbin kudade a kan harkokin tsaro irin na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari amma tambaya a nan shi ne ina kudadan suke.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: