Gwamnan Kano ya ja damarar samar da ruwan famfo

Gwamnan Kano ya ja damarar samar da ruwan famfo

Daga Wakilinmu

 

Gwamnatin jihar Kano, a karkashin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke taimaka wa manya da kananan kungiyoyin jihar musamman wajen ba su jari da kuma kudade da sauransu, mu ma muna neman irin wannan tallafi da gwamnan yake yi, kiran ya fito daga bakin shugaban kungiyar direbobin tankin ruwa na jihar Kano, Kwamared Aminu Almustapha, a lokacin da yake zanatawa da manema labarai kwanakin baya.

Kwamared Aminu Almustapha, ya ce babban taimakon da suke bukata daga wurin gwamnan a samar masu da wurin da za su rinka daukar ruwa da kuma kara ba su hadin kai da goyon baya a kan sana’ar ta su.

Shugaban kungiyar ya ce zuwa yanzu suna da mambobi a jihar kimanin 250 suna kuma ba shi hadin kai da goyon baya daidai gwargwado. Tun lokacin da Allah yasa ya zama shugaban kungiyar ya zo da tsaretsare masu muhimmanci wanda suke ciyar da kungiyar gaba da kuma mambobin ta.

Wadansu daga cikin tsare-tsaren sun hada da rarraba ruwa kyauta musamman yadda aka samu gobara a wadansu daga cikin kasuwannin Kano, shekarun baya. Shugaban ya kara da cewa, wadansu unguwannin cikin birnin Kano, da Rijiyar Lemo, Bachirawa, Tarauni da wadansu yanki na unguwar Birget sukan bayar da tallafin bayar da ruwan, sannan hatta gidajen gyara hali da kuma gidajen marayu sukan agaza.

Haka halin da ake ciki na Cobid 19 kungiyar yanzu haka ta himmantu wajen bayar da ruwa wanda suka fara tun kafin Azumin Ramadan har zuwa aiko da wannan labarin.

Kwamared Aminu ya ce wannan abu da suke yi ka da mutane su za ci cewa, gwamnatin jihar ta kasa ne wajen samar da ruwa ga al’ummar jihar, babu shakka gwamnan jihar na bakin kokarinsa wajen samar da ruwa ga al’ummar jihar. Wannan abu da suke yi har gidauniyar Dangote ta shigo inda suka hada kai da kungiyar inda suke rarraba ruwan kyauta a wadansu unguwannin da ke jihar.

Shugaban kungiyar ya yi kira ga attajiran jihar da su shigo domin taimaka wa al’umma da ruwa. Daga karshe ya ce daga lokacin da karagar shugabancin kungiyar ya samu nasarori da suka hada da samar da ofis ga kungiyar tare da samar mata da rijista tare da kulla dangantaka mai kyau tsakanin kungiyar da hukumar kashe gobara ta jihar kuma uwa uba gwamnatin jihar Kano inda har takardar girmamawa ta bai wa kungiyar da sauran takardun karrama wa daga wadansu wurare daban-daban a kasar nan har da kasar waje.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: