Yobe ta tallafa wa nakasassu da kayayyakin abinci

Hukumar bayar da agajin gag­gawa (SEMA) ta jihar Yobe, ta tallafa wa bangarorin na­kasassu a jihar fiye da 100 kayan abi­nci da na masarufi, a daidai lokacin ranar tunawa da ranar nakasassu ta duniya, wanda ya gudana a ‘yan kwa­nakin nan. 

 Yobe ta tallafa wa nakasassu da kayayyakin abinci

 

Sani Gazas Chinade Daga Damaturu

 

Da yake jawabi a lokacin kaddamar da rarraba kayan, babban Sakataren hukumar SEMA, Mohammed Goje, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ya bayyana cewa, hukumarsu ta ai­watar da shirin domin kara nuna yadda gwamnatin jihar, a karkashin gwamna Mai Mala Buni wajen ganin hannun jinkan ta ya kai ga kowa.

Dokta Goje ya bai wa wadanda suka ci gajiyar tallafin da cewa, gwamna­tin Alhaji Mai Mala Buni ta damu da matsalolinsu, sannan ya bukaci masu dauke da lalurar nakasassun da su yi amfani da kayan tallafin ta hanyar da ya dace.

A nasa bangaren, babban daraktan kungiyar fafutukar hakkokin jama’a ta ‘Network of Cibil Society Organi­zations’ (CSOs) a jihar Yobe, Alhaji Baba Shehu, ya yaba da wannan halin jinkai da gwamna Mai Mala Buni ya nuna wajen kula da halin da nakasas­su a jihar suke a ciki ta hanyar tallafa masu da kayan abinci da na masarufi.

Shi kuma shugaban kungiyar naka­sassu a jam’iyyar APC ta Arewa maso Gabas, Mohammad Abba Isa ya yaba da yadda gwamnatin Buni ke bai wa ya’yan kungiyarsu kulawa ta musam­man, sannan kuma ya bayyana cewa, za su yi amfani da kayan tallafin a hanyar da ta dace.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: