Saboda sa-in-sa:Matawalle ya yi sulhu da ‘yan jam’iyarsa ta PDP

Saboda sa-in-sa: Matawalle ya yi sulhu da ‘yan jam’iyarsa ta PDP

Shu’aibu Ibrahim daga Gusau 

An bayyana cewa, ya dace gwam­nan jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle ya dawo ya yi sulhu da ‘yan jam’iyyarsa ta PDP tun kafin rana ta fadi a shiga duhu.

Kalaman ya fito daga bakin daya daga cikin shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da ke jihar, Alhaji Anas Sani Anka, ya bayyana cewa, ya kamata gwamnati ta dawo ta taimaki mutanen da suka wahala da shi, duk wanda ka ga yana siyasa to yana yi ne domin ya ci riba.

Domin haka ya zama dole a mutunta mutanen da aka wahala da su, ya kara da cewa, da wadannan mutanen ba su ba shi dama ba, babu yadda za a yi kotu ta dauko shi ta ba shi kujerar gwamna.

Ya kara da cewa, ya dace a ce kashi sittin cikin dari na wadanda aka bai wa mukamai ya zama duk ‘yan cikin gidane, ya kara da cewa, wadanda gwamna Ma­tawalle ya dauko a matsayin kwamishi­noni kashi biyu bisa uku ba su cancanta ba, da za a yi amfani da ma’aunin da ya dace, ya ce, akwai bukatar sake duba tsarin da yabi wurin zabo su.

Ya ce, gwamnati ta dauko wadanda ba su san jiha ba ba su san matsalar ji­har ba, an wanke su an shafa masu mai an basu mukami, an ya ci gaba ake nema kuwa, ya kara da cewa, idan ka ga yaro a gida yana kokawa da rashin adalcin uba, to abin dubawa ne domin akwai rashin adalcin uban nan.

Anas ya kara da cewa, duk jam’iyyar da ta yi maka riga da wando ta tsaya aka zabe ka gwamna, to ya kamata a duba mata a taimake ta domin akwai wadanda aka wahala da su, domin haka kafin ka taimaki na waje ka taimaki na gida

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: