Masari ya karbi bakuncin shugaban majalisar dattijai

Masari ya karbi bakuncin shugaban majalisar dattijai 

 Rabiu Sanusi Daga Katsina 

 

Gwamna Aminu Bello Masari ya karbibakuncin shugaban Ma­jalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawal a masaukin gwamna da ke Abuja.

 

Shugaban Majalisar wanda ya sami rakiyar Sanata Ahmad Babba Kaita da Sanata Bello Mandiya, ya kawo ziyarar domin taya gwamna murna a kan na­sarar da ya samu a babbar Kotun koli ta kasa.

Bayan tafiyar shugaban Majalisar, sai gwamna Aminu Bello Masari, ya kai ziyara gidan Malam Mamman Daura, domin yi masa ta’aziyyar dan uwansa, Alhaji Abdullahi Dauda Daura wanda ya rasu ranar Talatar da ta gabata a Ka­duna, bayan gajeriyar rashin lafiya.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma al­barkaci abin da ya bari.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: