Hassan Abubakar III: Ya horar da matasa 450 kan sana’o’in dogaro-da-kai

Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Sakkwato ta Arewa da Sakkwato ta Kudu a Majalisar dokoki ta Tarayya Alhaji Hassan Bala Abu­bakar na III ya yaye matasa maza da mata su 450 ta fuskar koyar da su sana’o’i daban-daban domin dogoro da kai.

 Hassan Abubakar III: Ya horar da matasa 450 kan sana’o’in dogaro-da-kai

 

 Musa Lemu Daga Sakkwato 

 

Dan majalisar ya kashe zunzurutun kudi fiye da Naira miliyan 22 ta fuskar bayar da tallafi domin inganta matasan jihar domin hana su zaman kashe wando. 

 

A yayin da yake zantawa da manema la­barai da ke Sakkwato bayan yaye matasan a ranar Alhamis da ta gabata Alhaji Bala Hassan ya ce, an yi kokarin zakulo matasa mata 200 wadanda aka koyar da su harkar girke-girke da ba su atamfofi tare da basu kudi Naira dubu 10 kowannensu a matsayin tallafi.

Alhaji Bala Abubakar na III ya bayyana cewa, mazabarsa ya fitar da matasa maza da ke da hazaka su 250 wadanda aka koyar da su ayyuka iri daban-daban da suka hada da harkar noman shinkafa na zamani a inda aka hada kungiyoyi aka ba su buhu 10 na irin shinkafa tare da injunan ban-ruwa kazalika da kudi Naira dubu 10 kowannensu domin kwarin gwiwa.

Ganin yadda Bala Abubakar na III ya bayar da fifiko a kan harkar noma yasa mazabarsa ta ware zaratan manoman albasa su 275 a shekarar bana domin noman albasa tare da ba su gudunmuwar kudi Naira dubu 10 kowannensu domin kara ba su kwarin gwiwa.

Haka zalika Bala Hassan ya ce, nan ba da dadewa ba mazabarsa za ta mayar da hankali a kan noman alkama domin tab­batar da cewa, an samar da wadatar alkama a Sakkwato da za ta mamaye kasar nan.

Da ya juya ta fuskar zaizayar kasa da ke ci wa al’ummar jihar Sakkwato tuwo a kwarya ya ce, tuni wannan matsala ta zama tarihi ganin yadda aka shawo kan ta a dali­lin gabatar da korafi a gaban majalisa.

Har wayau cikin nasarorin da ya samu a shekaru 4 da suka gabata ya samar da riji­yoyin burtsatse guda 17 a yankuna daban-daban a inda gaba yake sa ran kara fiye da guda 4 domin amfanin al’ummar jiharsa.

Ana iya tunawa a shekarun da suka ga­bata, Alhaji Bala Hassan ya samar da gura­ben karo ilimi ga yara matasa maza da mata fiye da 300 domin karo ilimi a fannoni da­ban-daban da suka hada da fannin likita da injiniya da wadansu fanni ta koyon fasaha daban-daban .

A yayin da wakilinmu ya zanta da al’ummar jihar kan irin nasarorin da dan Majalisar Tarayyar, Alhaji Bala Hassan Abubakar na III ya samu sun bayyana cewa, babu wani dan Majalisa da ya cancanta ka­mar Bala Abubakar na III domin kasancew­arsa mutum haziki da ke da sanin ya kamata.

A zantawar da wakilinmu ya gudanar, ya hada da maza da mata a inda suka jinjina wa dan majalisar ganin yadda ya yi wa saura fintinkau wajen gudanar da ayyukan raya karkara da birane kazalika da kawo ci gaban al’ummar jihar Sakkwato.

Al’ummar Sakkwato suka bayyana cewa, dan majalisar ya taka rawar gani ya cancanci yabo tare da jinjina wanda ke nuna kulawa ga hakkin jama’a musamman talakawa da kananan yara.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: