Fatanmu yaranmu su tashi da tarbiyya -Hajiya Asama’u

Kungiyar (SA’ADAH CHILD ABUSE PREBENTION AWARENESS FOUNDATION) yankin Katsina ta gudanar da taron wayar wa da yara ‘yan firamare kai wajen ganin yadda ya kamata su kare kansu da kaucewa daga cin zarafin yara kanana da ke yawaita a yanzu.

Fatanmu yaranmu su tashi da tarbiyya -Hajiya Asama’u 

Rabiu Sanusi Daga Katsina

 

Taron wanda ya gudana a farfajiyar ajiye namun daji na Aldusar maklakar dan kasuwar nan watau Alhaji Usman Sarki da ke Katsina.

Akalla yara fiye 150 aka zabo daga makarantun firamare daban-daban a cikin birnin Katsina.

Tun farko dai an yi bayanai mabam­banta tare da jan hankali ga musamman yaran ta hanyar da za su bi su kiyaye daga mugun kudurin bata-gari.

Da take jawabi yayin gudanar da taron, shugabar kungiyar Hajiya Asma’u Ibrahim ta bayyana cewa, kungiyar ta kafu domin ganin sun wayar wa da kananan yara kai wajen kauce wa cin zarafi.

Sannan Asama’u ta kara da cewa, cikin kudurorin kungiyar su ne iliman­tar da yara, tare da nuna masu hanyoyin da za su bi domin kare tsiraicinsu tun suna kanana.

Sannan ta kara nuni da wuraren da yaran ya kamata su rufe tare da abubu­wan da ya kamata da ma hanyoyi domin fadawa da irin wadannan matsalolin cin zarafin yara.

Cikin wadanda suka gabatar da bayanai tare da jan hankali sun hada da Malam Surajo Farukh, inda yake cewa, yaran su tabbatar sun kara lura a duk lo­kacin da suka fito daga gida musamman mata, kada wani ya yaudare ta da misa­lin kudi ko halawa ya biya bukatar shi.

Ita ma Malama Basira Lawal AD, ta kara jan hankalin yaran da cewa, kada yaran su rinka fita ba tare da cikakkiyar shiga ta kamala ba.

Cikin karin bayanin da Hajiyar ta yi, ta bayyana cewa, yaran su rinka bayyana wa iyayensu dukkan wad­ansu bata-gari da ke yi masu magan­ganun banza da wadanda suka sabawa Addini.

Daga karshe Hajiyar ta kara jan hankali iyayen yaran wajen kula da su, tare da tuntubarsu halin da suke ciki na yau da kullum, sannan an nishadantar da yaran tare da gasa tsakaninsu da ya danganci wasa kwakwalwa, an yi fatan Allah ya mayar da kowa lafiya.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: