Fallasa: Faransa kanwa uwar-gamin rikicin Boko Haram

Hakika biri ya yi kama da mutum, rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa na ‘yan tayar da kayar baya a Arewa maso gabashin Nijeriya, kasar Faransa tana da han­nu a ciki dumu-dumu, wannan ko shakka babu. 

 

 

 Fallasa: Faransa kanwa uwar-gamin rikicin Boko Haram 

 

Idan muka waiwayi tarihi, za mu iya iske cewa, kasar Bir­taniya ita ta yi wa Nijeriya mulkin mallaka, a lokacin da suka kawo karshen daular Musulunci ta Usumaniyya, wad­da Shehu Usmanu Danfodiyo ya assasa, a shekara ta 1903.

Ita ma Faransa akwai kasashe a nan nahiyarmu ta Afirka ta Yamma wadanda ta yi wa mulkin mallaka fiye da wad­anda Birtaniya ta yi, domin kasashen Nijeriya da Ghana da Gambiya, su kadai Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka, a yayin da Faransa ta yi wa sauran masu yawa.

Ganin cewa, kasashen renon Birtaniya sun fi yawan jama’a da albarkatun kasa, a saboda haka Faransa ke yi wa Birtaniya bakin ciki, da hassada domin kada ta fi ta tara abin duniya, daga dimbin arzikin jama’a da na albarkatun kasa da Allah SWT ya huwace wa kasashe renon Birtaniya.

Baya ga wadancan dalilai, a takaice, game da jin haushin Birtaniya da Faransa ke yi, akwai kuma wadansu dalilai na boye birjik, sanin gaibu sai Lillahi.

A kwanan nan, shugabar wata kungiyar farar hula mai ra­jin kare hakkokin mata da kananan yara, Gimbiya Ajibola, ta jagoranci wani gangami na nuna rashin yarda da take-taken kasar Faransa a Nijeriya, inda a cikin jawabinta ta bankado tare da yin fallasa ga kasar Faransa, saboda bakar aniyarta ta wargaza tarayyar Nijeriya, ta hanyar amfani da ‘yan tayar da kayar-baya na ‘yan Boko-Haram.

A cikin jawabin Gimbiya Ajibola, ta nuna cewa, babu wani dalili da gwamnatin tarayya za ta zuba ido tana gani kasar Faransa tana keta mata diyaucinta, a matsayinta na ‘yantattar kasa, wannan abin kunya ne da ba zai sabu ba, bindiga a ruwa.

Ta ce, a shekarar da gwamnatin Buhari ta sami nasarar fatattakar ‘yan Boko-Haram ta hanyar sake kwato kananan hukumomi 60 da ke karkashin ikon ‘yan tayar da kayar-baya, abin bai yi wa kasar Faransa dadi ba, a saboda haka, ta sha aradun ci gaba da taimaka wa ‘yan Boko-Haram da bindigogi rantsattsu (AK 47) da miliyoyin alburusai.

Gimbiyar ta kara da cewa, shin sabon mulkin mallaka Faransa ke son yi wa Nijeriya, baya ga wanda Birtaniya ta yi, sannan ta ba mu ‘yancin mulkin kai, a shekara ta 1960, kuma aka sanya mu a jerin kasashen duniya masu diyau­ci. Idan kuma haka ne, me zai hana gwamnatin tarayya ta sanya wa Faransa takunkumin karya tattalin arziki, tare da yanke huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.

Fallasa: Faransa kanwa uwar-gamin rikicin Boko Haram 

Har ila yau, a cikin jawabin da ta yi cikin fushi, da nuna alhini ga mata, da kananan yara da rikicin Boko-Haram ya rarraba su da danginsu, Gimbiya Ajibola ta ce, kasar Far­ansa ta ware fiye da dalar Amirka biliyan 500 daga babban bankin kasar domin ci gaba da tallafa wa ‘yan ta’addar do­min su wargaza tarayyar Nijeriya.

Daga nan, ta takaita bayanin nata da cewa, cin kashin da kasar Faransa ke yi wa Nijeriya al’amari ne da majal­isar dinkin duniya, da kungiyar tarayyar Turai (EU) da ta Afirka (AU) da dangoginsu, idan ba su shiga sun yi uwa, sun yi makarbiya ba, rikicin Boko-Haram a Nijeriya kusan a ce ba ma a fara ba.

Gangamin nata ya tara daruruwan mata gwagware, wad­anda suka rasa mazaje, da kananan yara wadanda rikicin ya mayar da su marayu, ya rarraba su da mahallansu.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: