Babban burina tallafa wa al’umma — Galadiman Zazzau

 Babban burina tallafa wa al’umma — Galadiman Zazzau 

Isa A. Adamu Zariya

 

An yi kira ga al’umma, musam­man wadanda Allah ya ba su dukiya, da su rinka tal­lafa wa al’umma da dukiyoyinsu, ta kafa kamfanoni da samar da kananan masana’antu, domin kawo karshen matsalolin da suke addabar ‘yan Ni­jeriya, musamman matasa da suke kammala karatu, ba tare da sun sami aikin yi ba.

Galadiman Zazzau Alhaji Nuhu Aliyu Magaji ya bayar da shawarar jim kadan bayan kammala taro a hara­bar kamfanin NALMACO, da ya kafa domin tallafa wa al’umma, musam­man samar da ayyukan yi ga matasa da al’amurran da suka shafi kayayya­kin amfanin gona.

Galadiman Zazzau Alhaji Nuhu Aliyu ya ci gaba da nuna matukar damuwarsa na yadda a yau, al’umma da Allah ya azurta da dukiya, babu tu­nanin kafa ko da kananan masana’antu ne, sai dai kunshe kudi, ba tare da as­sasa wadansu abubuwa da al’umma za su amfana da rayuwarsu ba.

A cewar Galadiman Zazzau, mat­salolin durkushewar masana’antu da kuma kamfanoni musamman a jiho­hin Arewa, na matukar tayar masa da hankali, a dalilin ga matasa maza da mata, sun sami damar yin ilimi, amma babbar matsalarsu, rashin inda za su tsuguna, su sami yadda za su yi am­fani da iliminsu domin su rayu kamar yadda al’umma ke rayuwa.

A nan ne Galadiman Zazzau ya yi kira ga gwamnoni musamman na are­wacin Nijeriya, da su duba matsalolin durkushewar masan’antu da kamfano­ni, domin kawo karshen matsalolin da matasa da sauran al’umma ke ciki, na rashin ayyukan yi.

Alhaji Nuhu Aliyu Magaji Galad­iman Zazzau ya bayyana cewa, tun a shekaru da dama da suka gabata, ya kafa kamfanin da ake kira NALMA­CO, da nufin bayar da gudunmuwarsa ga rayuwar al’umma, musamman ma­tasa da kuma ganin an bunkasa noma ta samar amfanin gona ga kamfan­onin da suke ciki da kuma wajen Ni­jeriya.

Game da ayyukan da kamfanin NALMACO ya sa wa gaba kuwa, Galadiman Zazzau y ace, kamfanin NALMACO na tsayuwa irin na mai daka ga manonma, wajen tsaywa a wajen samun tallafin kudi, da zai tal­lafa ma su su yi duk noman da suke bukata daga cibiyoyin kudi , ko kuma babban bankin Nijeriya, wato CBN.

Galadiman Zazzau ya kara da ce­war, tsarin tallafa wa manoman, ba kudi ake ba manoman ba, amma a ka­rkashin tsarin da aka ambata, ko wane manomi, a dalilin tsayawar da kam­fanin NALMACO ta yi ma sa, za a ga ya yi noman da ya ke bukata, matukar ya cika sharuddan da aka gindaya ma sa.

A kuma tsokacin da Galadi­man Zazzau Alhaji Nuhu Aliyu ya yi kan wannan taro da kuma bay­anan da aka yi a wajen taron da suka fito daga wadanda suka suka yi jawabai a wajen taron, ya nuna matukar jin dadinsa na yadda aka nuna gamsuwa da yabo ga gareshi da kuma kamfanin NALMACO, na yadda suke tallafa wa manoma da kuma yadda kamfanin ke gudanar da ayyukansa bisa gaskiya, ba tare da sa wani tsabbare ba.

A kan haka ne ya ce, babu ko shakka, ya sami kwarin gwiwa na kara mike wa tsaye, wajen tallafa wa manoma da kuma ci gaba das a wan­nan kamfani bisa turbar da za a ci gaba da koyi da kamfanin wajen hulda da ayyukan da ake a cikin kamfanin.

Shi ko babban manaja mai kula da bayar da tallafi ga manoma na babban bankin Nijeriya [NIRSAL ], Alhaji Aliyu Abdulhamid, da farko ya bayyana Galadiman Zaz­zau Alhaji Nuhu Aliyu Magaji da c ewar, saboda tsarin rayuwarsa na ganin ya tallafa wa manoma, da kuma bin ka’idojin da babban bankin Nijeriya ta tsara, ya sa ka­mfanin NALMACO ya zama na farko da babban bankinNijeriya ya amince ya hada hannu da kamfanin NALMACO, domin aiwatar da tsarin tallafa wa manoma a karka­shin babban bankin Nijeriya.

A nan ne ya yi kira ga al’umma da su yi koyi da Galadiman Zazzau, wajen ganin sun yi amfani da damar da Allah ya ba su, wajen tallafa wa manoma, a shirin da babban bankin Nijeriya ya saw a gaba, na tallafa wa manoman Nijeriya.

Shi ko Alhaji Bala Shehu, babban manajan darakta na bankin STANBIC IBTC, da farko bayyana Galadiman Zazzau ya yi da cewar uba ne kuma wanda ya yi fice wajen ganin ya tallafa wa al’umma, ba a batun harkar noma ba, a cewarsa, ako wane bangare da al’umma ke bukatar tallafi, domin su inganta rayuwarsu.

A karshen jawabinsa Alhaji Bala Shehu ya lashi takobin yin duk mai

yiwuwa, na ganin bankin STAN­BIC IBTC, ya ci gaba da tafiya tare da kamfanin NALMACO, domin ganin manoman Nijeriya sun amfana da tal­lafin noma da babban bankin Nijeriya ke ba manoma, a karkashin NIRSAL da ta saw a gaba.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: