A ranar 1 ga Janairu, 2020: Sarkin Hausawan Gboko zai yi nade-naden sarauta 

A Ranar Laraba 1 ga Ja­nairu, 2020, mai gir­ma Sarkin Hausawan Gboko, jihar Binuwai, Alhaji Isa Bala Mamman Jagaba, zai jagoranci bikin nade-naden sarauta a fadarsa da ke garin na Gboko.

 

A ranar 1 ga Janairu, 2020:  Sarkin Hausawan Gboko zai yi nade-naden sarauta  

 

A wani bayanin da ya fito daga cikin daya daga cikin hakiman da za a nada, Alhaji Hamza Yahaya, ya bayyana cewa, ya rabauta da sarautar TAFIDA.

 

Da yake yin karin haske kan hidimomin da suka ra­taya a wuyansa a matsayin TAFIDAN sarkin Hausawan Gboko, Alhaji Hamza ya ce, sarautar Tafida, sarauta ce da akan bai wa ‘ya’yan sarakuna kuma ba ta da takamaiman ai­kin da Tafidan zai gabatar face wakiltar sarki a wurare na kusa da nesa, idan har sarkin ba shi da sukunin halarta da kansa da sauransu.

Alhaji Hamza Sabon Tafi­dan Sarkin Hausawan Gboko, an haife shi a shekara ta 1970, 1 ga Yuni, a unguwar Maruji cikin garin Mazoji, a karamar hukumar Matazu, jihar Kat­sina.

Tafidan ya sami zarafin yin karatun Arabiyya da Boko a matakai daban-daban, inda yake rike da takardar shai­dar ilimi ta Difloma wadda ya samo a kwalejin koyon shari’a da darussan Musu­lunci ta Misau, a jihar Bauchi kuma yana daya daga cikin ‘yan kasuwar da ludayinsu ke kan dawo tsakanin jihohin Binuwai da Filato da kuma Nasarawa.

Har ila yau, akwai Sardaunan matasa na sarkin Hausawan, watau Zakari Al­haji Abdullahi Babankaka, wanda kafin nadinsa yana daya daga cikin matasan da ke kula da lafiyar sarkin a fa­darsa da ke Gboko da kuma sanya ido kan mafi yawan hi­dimomin fada ciki har da kar­bar baki.

Daga cikin wadanda za a nada wa rawani, akwai Farfesa Alhaji Sharif Ari, na sashen tarihi, Jami’ar Maidu­guri wanda za a damka masa sarautar Zannan Sarkin Hau­sawan Gboko.

Da yake zantawa da Al­bishir, babban dan Zannan, watau Abdullahi Baba Sharif ya taya babansa murna tare da fatan Allah ya kama kuma a gama lafiya.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: