A Katsina: Masu fataucin miyagun kwayoyi sun shiga hannun hukuma 

A Katsina: Masu fataucin miyagun kwayoyi sun shiga hannun hukuma

Rabiu Sanusi Daga Katsina 

 

Hukumar yaki, sha da fa­taucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kat­sina, ta yi awan gaba da wadansu mutane 3 da zargin safarar miya­gun kwayoyi a karamar hukumar Bindawa.

Kwamandan hukumar Mista Sule Momodu ya bayyana haka a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Mista Musta­pha Maikudi ya rarraba wa mane­ma labarai.

Ya ci gaba da cewa, wadanda ake zargin a samu damar kama su a wurare daban-daban a yankin karamar hukumar Bindawa dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogi­ram 183.25 da wadansu kwayoyi daban-daban.

Sannan ya kara bayyana yun­kurin hukumar na kara kaimin kawo karshen sha da fataucin mi­yagun kwayoyi a jihar ya ba su damar baza jami’an su har lungu­nan jihar, ga shi yanzu haka sun yi nasarar cafke mutum 3 a wannan yankin.

Daga karshe bayanin ya kara tabbatar da cewa, wadanda ake zargin su ne suka addabi yankin karamar hukumar ta Bindawa wajen safarar miyagun kwayoyi.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: