A Damaturu: Dakarun soja sun fatattaki mayakan Boko Haram

A Damaturu: Dakarun soja sun fatattaki mayakan Boko Haram

Sani Gazas Chinade Daga, Damaturu 

Dakarun sojan kasar nan na sama da na kasa sun yi nasarar fatattakar mayakan da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne a harin da suka yi yunkurin kai wa garin Damaturu hedikwatar jihar Yobe da yammacin ranar Lahadin da ta gabata.

Kamar yadda mazauna ga­rin Damaturu ke cewa, may­akan Boko Haram, sun dumfari babban birnin ne ta mashigar hanyar Gashuwa wadda ta biyo kan hedikwatar ’yan sandan jihar da kimanin karfe 5:30 na yammacin ranar, wanda ya dauki fiye da awanni 2 ana musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da mayakan.

Bugu da kari kuma, ma­haran wadanda ke dauke da manyan makamai masu sarra­fa kansu da abubuwa masu fa­shewa, wadda cikin wani dan lokaci karar harbe-harbe da ta­yar da abubuwa masu fashewa ta hade garin Damaturu, lama­rin da ya razana jama’a tare da tilasta wa jama’a shiga gidaje su kulle; gudun abin da kan je ya dawo, kana daga bisani jami’an tsaron suka mayar da martani mai gauni ta hanyar taimakon rundunar sojojin sama.

Da yake tabbatar da afku­war lamarin a sa’ilin da luguden wutar ke wakana, mataimakin daraktan hulda da jama’a a runduna ta biyu ta lafiya dole, Kyaftin Njoka Irabor, ya kada baki tare da tabbatar da kawo harin.

Har wala yau kuma, jami’in yada labarai ya shaidar da cewa, jami’an suna samun galabar maharan, sannan kuma tuni maharan sun matsa daga inda suka yi tun da farko kan titin Gashuwa.

A hannu guda kuma, daru­ruwan matafiya ne wannan la­marin ya shafa, wadanda ke kan hanyar su zuwa Damaturu, babban birnin jihar Yobe; daga Maiduguri wadansu daga kan hanyar Gashuwa, a daidai loka­cin da bata-kashin ke gudana, haka nan kuma wannan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da dama kasancewar ranar ne ake cin kasuwar ta Damaturu.

A cikin matafiyan har da tawagar motocin gwamnan ji­har Borno Farfesa Babagana Zulum, kan hanyarsu domin dauko shi daga Gombe.

A nasa bangaren, gwam­nan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni, ya yaba da kokarin jami’an tsaro kan yadda suka mayar wa da maharan zazzafan martani tare da dakile aniyarsu na shigowa birnin Damaturu.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: