Shirin ginin Ruga zai lakume Naira biliyan 8.631 – Matawalle 

Shirin ginin Ruga zai lakume Naira biliyan 8.631 – Matawalle 

 Shu’aibu Ibrahim Daga Gusau 

 

Gwamnan jihar Zam­fara, Alhaji Bello Mu­hammad Matawalle ya bayyana cewa, gwamna­tinsa za ta kashe zunzurutun kudi har Naira Biliyan 8.631 wajen gina gidajen Fulani wanda aka fi sani da RUGA. Gwamnan ya bayyana hakan a cikin jawabinsa wurin bikin aza harsashin ginin ruga da ya gudana a garin Maradun, da karamar hukumar Zurmi da Maru, ya kara da cewa, bayan ginin Ruga gwamnati za ta sa­mar wa Fulani magani kyauta su da dabbobinsu.

Ya ce tsarin samar da magani zai gudana kamar yadda aka rinka gudanar da harkar hu­jin dabbobi a shekarun baya, domin haka ya ce, rugage za a rinka bi ana ba su magani.

Matawalle ya kara da cewa, domin rage cunkoso gwamna­ti ta umarci shugabannin ka­nanan hukumomi da su gina kananan rugage a kananan hukumominsu, da ke fadin ji­har.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, domin rage radadin talauci gwamnati za ta dau­ki matasa dubu uku, domin ba su kudaden tallafi duk wata, ya kara da cewa, ya bai wa shugabannin kananan hukumomi umarnin dau­kar ma’aikata dari 200 daga kowace karamar hukuma.

Idan ba a manta ba bikin aza harsashin gina ruga ya zo ne a lokacin da gwamnatin jihar take gudanar da bikin cika kwana dari a kan karagar mul­ki, wanda gwamnatin ta ware kwana biyar domin gudanar da bikin, za a kammala a ranar Juma’ar wannan mako.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: