NUP ta koka da rashin biyan hakkokin ‘yan-fansho- A Nijeriya

NUP ta koka da rashin biyan hakkokinyan-fansho  – A Nijeriya

 Sule Aliyu daga Bauchi 

 

 Kungiyar masu karbar fan­sho ta kasa (NUP) ta roki gwamnonin jihohi da su yi kokarin biyan basussukan giratuti da ake bin su, kana su waiwaya da bibiyar fansho duk bayan shekaru biyar-biyar.

 

A gefe guda, kungiyar ta jero wadansu daga cikin gwamnonin Arewa maso Gabas da suka fara ta­buka abin a zo a gani wajen biyan basussukan giratuti da ake bin su zuwa yanzu, kada su zama wadanda ba su motsa ba.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa, shiyyar Arewa maso Gabas, Alhaji Muhammad Inuwa Ahmad shi ne ya yi rokon a wata takardar bayani da aka rarraba wa manema labarai a Bauchi, yana mai cewa, masu amsar

fansho da suka sadaukar da karfinsu da lokacinsu wurin yin ayyuka tukuru ga jiho­hinsu suna tsananin bukatar gwamnatoci da su taimaki rayuwarsu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, a matsayin masu amsar fansho na dattawa, gwamnatoci daban-daban sun yi alkawuran cewa, za su biya su hakkokinsu idan suka samu zarafin darewa kan karagar mulki, domin haka suka ce akwai bukatar a cika wadannan alkawuran domin masu amsar fansho su ma rayuwarsu ta inganta.

A bisa haka, suka nuna kwarin gwiwarsu na cewa, gwamnatocin za su yi ko­karinsu wajen sauke basus­sukan giratuti da biyan fan­sho da ke kansu, a bisa haka suka nemi a rinka bibiyar kudaden da ake biya na fan­sho duk bayan shekaru biyar domin kyautata tsarin.

A cewar Alhaji Muham­mad Inuwa, “Yanzu haka wadansu gwamnonin are­wacin Nijeriya sun fara

hobbasa wajen biyan kudad­en giratuti da fansho, misali a jihar Bauchi, gwamna Bala Muhammad ya biya Naira miliyan 100 ga ‘yan fansho a watan Agusta, sannan a Sa­tumba ya sake biyan Naira miliyan 200 domin rage ba­sussukan fansho na kananan hukumomi da jihar, tare da tsammanin sake samun kaso mafi girma duk wata domin biyan wadannan basussu­kan,” A cewarsa.

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Bor­no, shi ma ya yi yunkuri mai kyau na biyan Naira biliyan daya a Yuli da Agusta domin biyan ‘yan fansho da suke jihar, tabbas da irin wannan kokarin za a iya kyautata harkar fansho sosai,” a ce­war sanarwar.

Mataimakin shugaban, ya kara da cewa, “Haka zan­cen yake, gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya biya Naira biliyan daya da miliyan dari ga ‘yan fanshon da suke bin gwamnatin jihar, muna fatan a yi irin wannan biyan ga ‘yan fanshon da suke kananan hukumomi su ma, muna da kwarin gwiwar cewa, kowane wata za a ke samun kason da ke fita, har ta kai ‘yan fansho suna cike da annashuwa a kowane lokaci, muna godiya,” A fadin sanar­war.

“Wani karin ci gaba, shi ma gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya biya Naira miliyan dari shida domin bi­yan basussukan giratuti,” a bayanin.

A gefe guda da yake jin­jina wa gwamnatocin da suka rage basussukan giratuti da ke kansu, Alhaji Muhammad Inuwa Ahmad ya bayyana gwamnonin jihar Adamawa da na Taraba a matsayin wad­anda har yanzu ba su samu kudaden giratutin da suke bi ba, yana mai fatan gwam­nonin za su motsa nan gaba kadan.

A cewarsa, akwai bukatar gwamnatoci suke duba halin da masu amsar fansho ke ciki domin ky­autata masu rayuwa, a ce­warsa dattawa ne wadanda suke neman agaji biyo bay­an kammala ayyukan raya jihohinsu da suka yi.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: