Mun yi rashin Hajiya Binta Dangida

Mun yi rashin Hajiya Binta Dangida

Mun yi rashin Haji­ya Binta Dangida a ranar 26 ga Sat­umba, 2019 bayan fama da doguwar jiyya.

Ta rasu tana da shekaru 75, a Asibitin kwararru na Muhammad Abdullahi Wase da ke unguwar Tura­wa ta Nassarawa.

Ta rasu ta bar ‘ya’ya 8 daga cikinsu akwai Aliyu M. Dangida wakilin jaridar Banguard a jihar Jigawa da Dokta Musa Suleiman Jibia, shugaban bangaren kula Injiniyanci na lantarki a Kwalejin fasaha ta Has­san Usman Katsina da ke Katsina da Umar Farouk na Jami’ar Tarayya da ke Du­tse ta jihar Jigawa da sau­ransu.

Har ila yau marigayiyar babbar ya ce ga Dokta Aliyu Abdullahi Jibia na bangaren kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero Kano da Alhaji Garba A. Dangida mawallafin mujallar News­week.

Tuni aka yi jana’izarta a makabartar Bachirawa da ke karamar hukumar Dala ta jihar Kano.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: