Bauchi za ta inganta gasar karatun alkur’ani –Shugaba

Bauchi za ta inganta gasar karatun alkur’ani –Shugaba

 

Sule Aliyu Daga, Bauchi

Kwamishinan kula da har¬kokin addinai na jihar Bauchi, Alhaji Ahmad Aliyu Jalam ya jaddada kudirin gwamnati na goyon bayan har¬kokin addinai a jihar.

Jalam ya furta hakan yayin zanta wa da manema labarai a kan shirye-shiryen jiha kan gasar karatun Alkur’ani da za a yi a kananan hukumomi 20 da ke Bauchi, kwamishinan ya jad¬dada muhimmancin Alkur’ani a matsayin littafin shiriya da yake shiryar da al’umma ya bayar da tabbacin goyon bayan gwamnatin jiha ga dukkan yankunan ka¬nanan hukumomi 20 da ke fadin jihar domin samun nasarar gasar a jiha baki daya.

Kwamishinan ya bayyana cewa, gwamnati ta kara fadin ma’aikatan ta da nufin inganta ayyuka inda aka kara masu da sashen jin dadi da walwalar jama’a da hukumar kula da Ma¬rayu da marasa galihu, da huku¬mar Shari’a na jiha da hukumo¬min aikin Hajji na Musulmi da Kirista.

Sai ya bayyana kudirinsa na yin aiki tukuru a dukkan wad¬annan sassa domin samun na¬sara da ci gaba mai dorewa da ma’ana a jihar.
Da yake zantawa da mane¬ma labarai a ofishinsa, shuga¬ban kwamitin gasar karatun Alkur’ani na jihar, Malam Mus¬tafa Baba Ilelah ya yi alkawarin inganta gasar karatun alkur’ani a jihar ta yadda masu gasar za su rinka yin koyi ta hanyar aikata abubuwan da alkur’anin yake umarni da yi.

Malam Mustafa ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, ya ce, bayan mun zauna mun yi nazari sai muka kudiri ani¬yar kaucewa kura-kuran da aka samu a baya, kuma muka yi niyyar inganta gasar karatun alkur’anin ta yadda mahalarta gasar za su rinka kokarin dabbaka abubuwan da alkur’anin yake koyarwa, ba ya zama mu¬tum yana karanta Alkur’ani ba ya aiki da shi ba domin an ce sau da yawa za ka samu mutum yana karanta alkur’ani amma ba ya aiki da shi, shi kuma alkur’ani yana la’antarsa.

Shugaban ya bukaci ma¬halarta gasar da daukacin al’ummar Musulmi da su guji aikata abubuwan da Allah ya hana su kuma rinka aikata ayyu¬kan alheri suna yin umarni da shi domin samun dacewa a ranar kiyama.

Ya ce, suna kan shirye-shir¬ye domin ganin sun fara gudanar da gasar karatun alkur’anin a dukkan kananan hukumomin jihar, kafin wadanda suka zama zakaru su wakilci kananan huku¬mominsu a gasar jiha, wanda za a yi a karamar hukumar Ningi.

Shugaban ya ce, a bana za su yi kokarin shiga dukkan lun¬guna da sako na jihar domin dada wayar wa masu makaran¬tun haddar alkur’ani da masu makarantun alkur’ani da sauran al’ummar Musulmi kai dangane da gasar da zakulo hazikan ma¬haddata da makarantun alkur’ani da za su shiga cikin gasar.

News Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: